Jawabin Tinubu: Babu wani kuɗin tallafi da aka raba wa jihohi — Gwamnan Oyo

Tinubu ya ce an raba wa jihohi N570bn don tallafa wa jama’a kan ƙuncin rayuwa.

Jawabin Tinubu: Babu wani kuɗin tallafi da aka raba wa jihohi — Gwamnan Oyo

Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya ce sabanin ikirarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi, Gwamnatin Tarayya ba ta raba wa jihohi naira biliyan 570 domin tallafa wa jama’a ba.

Yayin jawabinsa na kwantar da hankalin al’ummar ƙasar da ke zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta raba kuɗin ga gwamnonin jihohin ƙasar 36 na ƙasar, domin sauƙaƙa wa jama’a matsin rayuwa.

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kuma bai wa ƙananan harkokin kasuwanci 600,000 tallafi, sannan kuma akwai wasu ƙarin ƙananan sana’o’in 400,000 da za su amfana da tallafin su ma.

Sai dai cikin wani dogon wani saƙo da Gwamnan na Oyo ya sanya a shafinsa na X a ranar Alhamis, ya ce shi dai jiharsa ba ta san da wannan kuɗi da Tinubun ya ce gwamnatinsa ta raba wa jihohi ba.

Gwamnan ya ce yana mayar da martani ne kan maganar da wani ɗan jiharsa ya yi kan iƙirarin Gwamnatin Tarayyar cewa ta raba wa jihohi sama da naira biliyan 570 domin tallafa wa jama’a kan ƙuncin rayuwa.

A cewar Makinde, “maganar na daga irin batutuwan da Gwamnatin Tarayyar ke yi ne na faɗin abin da ba haka yake ba.

“Kuɗaden da ake magana na daga cikin rancen Bankin Duniya na shirin NG-CARES, wanda kuɗi ne da ake tallafa wa jihohi wajen farfaɗowa daga annobar Korona, inda jiha za ta yi amfani da kuɗinta ta aiwatar da shirin, daga baya kuma Bankin Duniya ya mayar mata da kuɗin ta hanyar Gwamnatin Tarayya bayan bankin ya tantance abubuwan da jihar ta yi da nasarorin da ta samu.

“Ya kamata ma fa a sani cewa kuɗin na Dankin Duniya bashi ne ga jihohi ba tallafi ba, saboda haka jihohi za su biya kuɗin.

Gwamnan ya ce jiharsa, Oyo, ta samu kuɗin ne, kashi biyu, inda a kashin farko aka ba ta naira biliyan 5.98, sannan a kashi na biyu ta samu naira biliyan 822.

“Saboda haka a taƙaice gwamnatin tarayya ba ta ba jihar Oyo wani kuɗi ba.

Makinde shi ne gwamnan jam’iyyar PDP, na biyu da ya soki Tinubu a kan jawabin a kwanakin nan.

Ana iya tuna cewa a bayan nan ne Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ce jawabin shugaban soki-burutsu ne kawai — kuma fanko ne — da babu abin dauka a cikinsa.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna