Jawabin Tinubu ya nuna akwai mafita game da matsalolin Najeriya — Jigon APC

Jigon ya ce Tinubu ya damu matuƙa game da halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Jawabin Tinubu ya nuna akwai mafita game da matsalolin Najeriya — Jigon APC

Jigo a jam’iyyar APC, Nasiru Bala Aminu Ja’o’ji, ya ce jawabin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, ya nuna akwai mafita game da matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Ja’o’ji, ya bayyana hakan ne sa’o’i kaɗan bayan da Shugaban ƙasa ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi kan zanga-zangar da ake yi kan halin yunwa da ake fuskanta.

An shirya gudanar da zanga-zangar har tsawon kwanaki 10 amma daga bisani ta rikiɗe zuwa tashin hankali.

Zanga-zangar ta kai ga lalata dukiyoyin jama’a da na gwamnati, abin da ya zama barazana ga zaman lafiya a was jihohin Najeriya.

Yayin da yake yaba wa shugaban ƙasar kan matakin da ya ɗauka na yi wa ƙasar jawabi, Ja’o’ji ya ce, “Jawabin Shugaban ƙasa ya nuna ƙoƙarin gwamnatinsa na kawo sauƙi ga rayuwarmu.

“Jawabin Shugaba Tinubu ya nuna yadda yake bin dimokuraɗiyya da jin-ƙan talakawa a matsayinsa na shugaba. Nasarorin da wannan gwamnati ta samu sun bayyana yadda ta ke ta ɗauki gaɓaran jagoranci nagari.

“Muna gode masa kan gane haƙƙin mutane na bayyana damuwarsu yayin da yake jaddada muhimmancin kare rayuka da dukiyoyi. Wannan shi ne jagoranci na gaskiya.”

Ya yaba wa Shugaba Tinubu kan nuna damuwarsa game da ɓarnar da aka yi a jihohin Borno, Jigawa, Kano, da Kaduna.

“Yana da kyau a gane cewa kuɗin biyan bashin Najeriya ya ragu daga kashi 97 na jimillar kuɗaɗen shiga zuwa kashi 68 cikin watanni 13 da suka gabata ƙarƙashin Shugaba Tinubu. Wannan shi ne jagoranci.”

Ya ce gwamnatin tarayya ta samu dala miliyan 620 domin amfani da su wajen samar wa matasan Najeriya miliyan uku aikin yi.

Ja’o’ji, ya buƙaci masu zanga-zangar da su duba irin jajircewar gwamnatin Shugaba Tinubu tare da buɗe ƙofar tattaunawa don samun mafita game da halin da ake ciki a ƙasar nan.