Jega ga majalisa: Ba ja da baya kan amfani da na’ura
Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya tsaya kai da fata cewa hukumar ba za ta sauya ra’ayinta kan amfani da na’ura wajen tantance masu jefa kuri’a ba a zaben da za a gudanar a watan gobe. Farfesa Attahiru Jega ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa […]
Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya tsaya kai da fata cewa hukumar ba za ta sauya ra’ayinta kan amfani da na’ura wajen tantance masu jefa kuri’a ba a zaben da za a gudanar a watan gobe.
Farfesa Attahiru Jega ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa a shekaranjiya Laraba, inda ya shaida wa majalisar cewa amfani da na’urar zai taimaka wajen magance magudin da ’yan siyasa za su shirya tare da hadin baki da ma’aikatan INEC a rumfunan zabe.
Farfesa Jega wanda ya karanto sassa da daman a tsarin mulkin 1999 da dokar zabe ta 2010, ya ce Hukumar INEC ba ta saba wa doka ba wajen yin amfani da na’urar don tantance masu kada kuri’a.
Ya ce, sashi na 52 (2) na dokar zabe yana magana ne kawai kan kada kuri’a da amfani da na’ura mai aiki da lantarki wajen jefa kuri’a.
Ya ce, dimbin masu kada kuri’a daga jihohin Adamawa da Yobe da Borno sun samu katin zabensu na dindindin a kan lokaci saboda jihohin Adamawa da Yobe na cikin jihohin da aka fara aikin gwajin raba katunan da hukumar ta gudanar a sassan kasar nan.
Game da rahotannin cewa ’yan siyasa na sacewa ko sayen katunan zabe, Farfesa Jega ya ce, “Duk wanda ya saya ko ya sace katin ba zai iya amfani da shi wajen zabe ba, don haka babu amfanin hakan.” Ya ce a kwanan baya, an sace katunan zabe dubu uku daga hannun ma’aikatan INEC a Jihar Ebonyi.
Game da yiwuwar ko za a sake dage zaben, Farfesa Jega ya ce yin hakan ya saba wa tsarin mulki domin lokacin da doka ta sahale wa hukumar zai cika ne a watan Afrilu. Jega ya ce babu dan Najeriya mai kishin kasa da zai yi tunanin sake jan kafa wajen gudanar da zaben.
Sai dai ya ce tsakanin katin zabe dubu 800 zuwa miliyan daya ne har yanzu ba a buga sub a, amma ya tabbatar cewa suna kan aikin buga su kuma nan da kankanen lokaci za a raba wa masu zabe.
Da sanatocin suka matsa masa kan idan a karshen mako shida hafsoshin tsaro suka bukaci a kara wa’adin lokacin zaben, me shi da hukumarsa za su yi, Farfesa Jega ya ce ba zai yi magana a madadin hafsoshin tsaron ba, domin lamarin tsaro bai cikin ikon INEC a matsayinta na mai shirya zabe.
A ranar Talata ce Majalisar Dattawa ta gayyaci Jega bayan gabatar da bukatar haka da Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Sanata bictor Ndoma-Egba ya gabatar, inda ya yi zargin cewa amfani da na’urar tantace masu zabe ya saba wa dokar zabe.
Darakta Janar na Kwamitin Kamfe din Shugaba Jonathan, Ahmadu Ali ya bukaci a yi watsi da amfani da na’urar tantance masu zabe a lokacin zabe.