Jelen jalauta jari
Jelen jalauta jari al’amari ne da kowane dan kwadago mai neman kwadago ke aiwatarwa, musamman idan an biya shi ladar kadago, bayan ya gogu da gumurzun aiki. Su kuwa masu hada-hada a kasuwanni, sukan yi jelen jalauta jinjirin jarinsu ne, in sun samu kayayyakin bukatun al’umma da sukan baje wa masu neman irin hajar da […]
Jelen jalauta jari al’amari ne da kowane dan kwadago mai neman kwadago ke aiwatarwa, musamman idan an biya shi ladar kadago, bayan ya gogu da gumurzun aiki. Su kuwa masu hada-hada a kasuwanni, sukan yi jelen jalauta jinjirin jarinsu ne, in sun samu kayayyakin bukatun al’umma da sukan baje wa masu neman irin hajar da ta yi daidai da bukatunsu na yau da kullum. Sai dai wani babban tasgaro da ya jefa Haurobiyawa cikin gogoriyo, shi ne ’yan bumburutu masu buruntun satar mai sun sanya kayan masarufi sun tsula tsadar tsiya, a daidai lokacin da albarkatun man tunkuza suka yi rugu-rugu a kasuwanni duniya.
A rana ta karamin lauje da karamin lauje na watan Dashen-baba na shekarar dubu karamin lauje da sili da babban lauje, Baban-burin huriyyar Haurobiyawa ya gabatar da baje-kolin Hauro na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, ta yadda za mu samu damar yin sama-sama da matsalolin rayuwa mu kwala su da kasa. Waje-kolin na Hauro an ce zan hauro wa Haurobiyawa da damin Hauro har tiren-taliya manuniyar sama, sabanin yadda aka rika yayatawa cewa, za a sulalo mana da Hauro tiren-taliya tukunyar dambu, don mu dambace da matsalolinmu. Babban abin takaici shi ne, kamata ya yi a ce yadda man tunkuza ya yi rugu-rugu a fadin duniyar nan, to Haurobiyawa ma su samu saukin sayensa, tunda a kasarsu ake tono shi, a kogi ko tundurkin tudun kasa. Yanzu kowa ya san kudin jelen jalauta jari ya tsawwala, har ta kai ga al’umma sun kasa yin walwala.
Mahukuntan Haurobiya a karkashin jagorancin jam’iyya mai maganin zogi da radadin kurungu, ta samu jibgin sharar matsalolin rayuwa da suka dabaibaye Haurobiyawa, shi ya sa dole sai an sanya tsintsiya mai kwakwa an share duk wata jiba da Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta jibga wa al’ummar kasar nan tsawon shekaru sili da manuniyar sama. Kuma daukacin baje kolin Hauron da aka sha gabatarwa a majalisar Haurobiya ba mu da tabbacin an aiwatara da su, don fitar da al’umma daga kangin wahalhalun rayuwa, tunda suka kasa nemo ruwayar da zai taimaka musu wajen gyara, sai ma a karshe suka karke da ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege.
’Yan makaranta ya kamata mu fasko cewa, karairayewar farashin albarkatun tunkuza a duniya bai kamata ya jefa mu cikin rukwatubo ba. Domin yau a Hadaddiyar Daular Larabawa har ragowar farashi ake yi. Ko hakan ya auku ne saboda mu ba Hadaddiyar Daular Haurobiyawa ba ce kasarmu? Amsar dai ita ce mu bibiye kadin yadda muke tsuwurwurta ayyuka a kasarmu ta haihuwa.
To, ga shi kuma kasar Sin ta bijiro da tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikinta na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, inda ta bijiro da manufofin zabge haraji da tallafa wa wasu masana’antu da bayar da dimbin taimako ga raunanan talakawan Sinu, don hana yin sane.
Idan Haurobiyawa suka yi la’akari da wadannan dabarun Sinawa, za su tabbatar da cewa, Shugaban kasar Haurobiyawa ya canko wasu daga cikin wadannan dabarun Sinawa. Idan kuwa haka ne, ta yaya za mu more lagwadar wannan baje kolin Hauro, ta yadda za mu samu maganin haure-haure da hauragiya a kasar Haurobiya?
Batu na ingarman karfen karafa, wajibi ne kowane Bahaurobiye ya tunkari aikinsa na laluben na-koko wajen sarrafa katako, amma ban da barace-barace da dan koko, musamman ma jin cewa, za a jinka wa raunana Hauro dubu babban lauje tsakanin shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama zuwa ta dubu karamin lauje da sili da tukunyar dambu.
Bayanin baje kolin kasar Haurobiya na nuni da cewa, Baban-burin-huriyya ya canko dabarun Sinawa, amma bai zakulo na Hadaddiyar Daular Larabawa ba. Don haka Haurobiyawa sai mu himmatu wajen aiwatar da dabarun ririta abin hannu. Kuma kowa ya yi kwadago don neman kadago, amma ban da darewa bisa katanga kamar Gizo-gizon dakin-gwaggo. Uwa-uba, dole ne mu taimaka wa gwamnatin Haurobiya, wajen yin tonon silili ga ’yan bumburutu, masu buruntun satar mai, domin su ke tsawwala mana hauhawar farashin jelen jalauta jari. Sannan mu duba yiwuwar tursasa Gwamnatin Haurobiya ta daina ba mu sudin albarkatun man tunkuza. A da na taba rokon marigayi Shugaba ’Yar’bishiya kan lallai ya samma mana sudi, har ta kai ga ya zabtare farashin albakatun man zuwa Hauro manuniyar sama da babban lauje, amma da shugaban gudun-loko da Jona-tantin mulki ya kama ragama sai kawai ya tsawwala farashi. Jelen jalauta jari dai ya zama jalli-joga, har a kurtun magana na halo-alalo, musamman ma ganin an yanka wa Kamfanin yin batu a kurtu na Maman-tine harajin tiren taliya kudi barkatai. Ga berayen da suka yi sama da fadi a cinikin kayan artabun baraden Haurobiya. Tuni dai aka damke su Samun-bom Da-sauki da Baffan-rawa da Malam Namuduka da sauransu.
Lallai muna bukatar saman-dagarin samarin kusu, mu kuma hana mata irin su Mace-da-zane da In-gwangwaje-in-wala rawar gaban hantsi. Batun mai dan boto kuwa da take cewa, baje kolin Hauron bana damfara ne, ba ma bukatar mayar musu da martani, domin mun san ‘kura ba za ta ce da kare maye ba.’ Kowa ya san jiga-jigan mai dan boto su ne gwanayen damun-fura a damfara da yawon-dara a wajen yaudarar al’umma. Miyagu ku bibiyi mugun aikinku.
Haurobiyawa mu hada karfi da karfe wajen tabbatar da tsare-tsaren kawo sauyi da aka bijiro da su a cikin kundin baje-kolin Hauro na bana, musamman don mu more lagwadar dama-dama-da-kurda-kurdar wasan Samson siya-siya. Kada mu bari a maimaita Damo-da-kura-diyya. Da zarar mun yi sakaci, to za a bar mu da cin yadiya, ko kuma gumurzun dundume kururu da gwazarma, sai dai in rama da garin gero sun yi kawance, sannan mu samu dundume tunbinmu da rummace.