Jemagu: Garin da maza ba su auren macen da ta wuce sakandare a Kano
Na yi imani cewa duk yayin da lokacin aurena ya yi Allah zai kawo min miji.
Tun da dadewa aka bayyana ilimin ’ya’ya mata a matsayin wani bangare na ci gaban al’umma wanda yake samun tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu a ciki da wajen kasar nan don karfafa gwiwar al’umma a kan lamarin.
Sai dai duk da irin wannan tagomashi, ilimin matan har yanzu yana fuskantar kalubale musamman a Arewacin kasar nan inda ake alakanta hakan da addini da al’ada da sauransu.
A yanzu haka al’ummar garin Jemagu a Karamar Hukumar Warawa a Jihar Kano, yara mata ba su yin karatun da ya wuce sakandare saboda idan har suka yi karatu mai zurfi sukan fuskanci matsala wajen yin aure domin mazan garin ba sa auren macen da ta yi karatu fiye da sakandare.
- Yadda Arsenal za ta iya lashe Firimiyar Ingila
- Kashi 28.5 na Kanawa na fama da hawan jini — Kwamishinan Lafiya
Mazan garin Jemagu sun yi imanin cewa matan da suka yi karatun gaba da sakandare idonsu na budewa yadda maza ba su iya juya su ba.
Mutanen garin sun bayyana cewa ilimin ’ya’ya mata yana farawa ya kare a makarantar firamare da sakandare.
Babangida Adamu yana daya daga cikin mazan garin Jemagu, wanda ya yi imanin cewa bai kamata mutum ya auri macen da ta yi karatu fiye da sakandare ba.
Ya kara da cewa matan da suka yi karatu mai zurfi ba su son auren mazan da ba su da ilimin boko.
“Maganar gaskiya duk macen da ta yi karatu mai zurfi ba ta son auren mutumin da ba ya da ilimi mai zurfi.
“Ni ba zan auri macen da ke da digiri ba bayan ni ba ni da digiri. Hakan ya sa maza da yawa ba su son auren macen da ta yi zurfi a karatu,” in ji shi.
Sai dai Khadija Muhammad Jemagu mai shekara 25 da haihuwa wacce a kwanan nan ta haɗa karatun difloma a bangaren kasuwanci a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Kano, ta ce ta yanke shawarar taimaka wa kungiyoyi masu zaman kansu don bunkasa ilimin ’ya’ya mata a yankinsu.
Ta bayyana cewa akwai bukatar a wayar wa iyaye kai a kan muhimmanci ilimin ’ya’ya mata.
A cewar Khadija mutane da yawa sun faɗa mata cewa tunda ta zaɓi ilimin boko zai yi wahala wani namiji ya zo kusa da ita, domin mazan suna ɗaukar cewa ta fi su wayewa saboda ba su yi karatu mai zurfi ba.
Ta ce, “Tun kafin na kammala difloma mutane da yawa sun yi ta zunden mahaifina cewa tunda ya zaɓi ya sanya mu a makaranta, za su ga mutanen da za su zo su aure mu.
“Fiye da shekara bakwai nake zaune a haka.
“Babu namijin da ya taba zuwa wurina da maganar aure, ba don komai ba sai don ina da difloma.”
Sai dai duk da haka wasu ’yan matan da suka haɗa da Hassana Muhammad suna nan suna ƙoƙarin samun takardar shaidar samun horon a bangare koyarwa.
Amma har yanzu babu na namijin da ya nuna sha’awar aurenta a yankin. Ita ma ta dage cewa ilimi shi ne abu mafi muhimmanci a wurinta.
Haka Hassana ta hakikance cewa wata rana za ta samu miji a ciki ko wajen garinsu.
Ta sha alwashin cewa babu wani zagi ko kyama da za su karya gwiwarta daga neman ilimin da ta sa a gaba “Bayan na gama karatun sakandare sai na fara karatun NCE a nan garin Warawa, to, sai dai kun san yadda tunanin mutanenmu yake.
“Suna kallonmu a matsayin karuwai. Babu wanda ya zo neman aurenmu. Sai dai ni hakan ba zai karya min gwiwa daga neman ilimin da nake yi ba. Na yi imani cewa duk yayin da lokacin aurena ya yi Allah zai kawo min miji,” in ji ta.
Zainab Makera ta yi aure bayan ta kammala karatunta na sakandare sai dai ta ce tana so ta ci gaba, amma abin ya zame mata wahala, domin dole ta zabi daya ko aurenta ko kuma karatu.
Ta bayyana cewa tana ta kokarin ganar da mijinta don ya kyale ta ci gaba da karatunta, sai dai ya fada mata cewa idan tana son ci gaba da karatu sai dai ya sake ta.
Wasu ’yan kadan daga cikin matan garin da suka yi nasarar shawo kan mazansu suka yarda suka ci gaba da karatunsu, “suna nan suna fuskantar rashin amincewa daga al’ummar yankin,” in ji Hassana.
Hukumomin ilimi a Karamar Hukumar Warawa sun nuna cewa ba wannan tunani ne kadai abin da ke ci wa harkar ilimin ’ya’ya mata a Jemagu tuwo a kwarya ba.
Rashin bayar da hadin Kai daga iyaye musamman iyaye mata shi ne abin da ke kara tabarbarewar al’amuran.
“Akwai wasu dalilan da suke hana mata zuwa makaranta. Kadan daga ciki sun hada da halayyar da iyayensu ke nunawa musamman iyaye mata, inda suke dora wa yaran talla da sauran ayyukan wahala da ke hana su zuwa makaranta,” in ji Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Warawa, Munir Muhammad.
A kan batun samun mazan aure ga matan da suka yi karatu mai zurfi a Jemagu, Munir ya ce wannan matsalar ba kawai a Jemagu ko Warawa kadai take ba, aba ce da ta shafi Arewacin Najeriya gaba daya inda ake samun maza musamman wadanda suka yi ilimi mai zurfi suna kyamar auren matar da ta yi ilimi mai zurfi.
Ya kara da cewa gwamnati na aiki da Kungiyar Iyaye da Malamai (PTA) da iyaye mata da sauran masu ruwa-da-tsaki don bunkasa ilimin ’ya’ya mata a karamar hukumar.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa baya ga talauci da ke damun al’ummar yankin, rashin wayar da kai da rashin isassun makarantu da matsalar ruwa a Jemagu ne ketilasta yara musamman mata ba su zuwa makaranta domin sai sun yi tafiya mai nisa za su debo ruwan da za a yi amfani da shi a gida duk da cewa gwamnati ta yi alkawarin matsalar ruwa za ta zama tarihi a yankin.
Sun kuma bayyana kyamar da maza ke nuna wa matan da suka yi karatu mai zurfi a matsayin babbar matsalar da ke ci wa harkar ilimin ’ya’ya mata tuwo a kwarya a garin.
Shugaban Riko na Karamar Hukumar, Lamido Sanusi ya bayyana cewa batun rashin ruwa ma babbar matsala ce a garin Jemagu.
Ya bayyana cewa burinsu shi ne mata su samu ilimi tun daga firamare har zuwa jami’a ba tare da nuna kyama a Jemagu ko kuma sauran garuruwa da kauykan da ke Karamar Hukumar Warawa.
Aminiya ta gano cewa matsalar da ’yan matan ke haduwa da ita ta rashin samun mijin aure bayan sun kammala karatu a manyan makarantu na ci gaba da sare gwiwar iyaye wajen tura ’ya’yansu don su fadada ilimi musamman da yake mazan ma ba su fiye zarce karatun sakandare ba.