Jerin ƙasashe 24 da suka yanki tikitin Gasar AFCON 2025
A wannan makon ne aka kawo ƙarshen fafatawar neman gurbi a Gasar Kofin Nahiyar Afrika ta 2025, inda dukkanin tawagogi 24 da za su kece raini a gasar suka bayyana. Yayin da wasu tawagogin suka samu cancantar shiga gasar tun da fari, saura irinsu Jamhuriyar Benin sun samu nasu tikitin shiga gasar ne a ƙurarren […]
A wannan makon ne aka kawo ƙarshen fafatawar neman gurbi a Gasar Kofin Nahiyar Afrika ta 2025, inda dukkanin tawagogi 24 da za su kece raini a gasar suka bayyana.
Yayin da wasu tawagogin suka samu cancantar shiga gasar tun da fari, saura irinsu Jamhuriyar Benin sun samu nasu tikitin shiga gasar ne a ƙurarren lokaci.
- Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sabon Babban Hafsan Sojin Ƙasa
- Tabbas akwai yunwa a Najeriya amma komai zai daidaita — Tinubu
Gasar dai za ta gudana cikin watan Disamba mai zuwa a ƙasar Morocco, inda mai masaukin baƙin ta samu gurbin shiga gasar kai tsaye.
Sai dai wasu daga cikin manyan tawagogi irinsu kasar Ghana ba za su samu shiga gasar ba wacce ake sa ran manyan ƙungiyoyi irinsu Najeriya da Masar da Afrika ta Kudu da Tunisia, da masu riƙe da kofin a halin yanzu Ivory Coast na cikin ƙasashen da za su fafata a gasar ta ƙungiyoyi 24.
Ga cikakken jerin sunayen tawagogin da suka samu nasarar shiga Gasar AFCON ta 2025:
1. Algeriya
2. Angola
3. Jamhuriyar Benin
4. Botswana
5. Burkina Faso
6. Kamaru
7. Comoros
8. Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo
9. Masar
10. Equatorial Guinea
11. Gabon
12. Ivory Coast
13. Mali
14. Mozambique
15. Najeriya
16. Senegal
17. Afirka taKudu
18. Sudan
19. Tanzaniya
20. Tunisiya
21. Uganda
22. Zambiya
23. Zimbabwe
24. Moroko
CAF ta fitar da ’yan wasan da take takarar gwarzon bana
A makon jiya ne kuma Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nahiyar Afrika (CAF) ta bayyana sunayen gwarazan ‘yan wasa 5 a ajin maza a hukumance domin fafatawa wajen lashe kyautar gwarzon dan wasan caf ta 2024.
A yayin dan wasan gaban Najeriya Ademola Lookman ya samu shiga cikin gwaraza 5 din, jagoran tawagar kasar, William Troost-Ekong bai samu shiga cikin jerin sunayen mutum 9 na farko ba.
An tsara bikin bada kyautar gwarzon caf din ta bana ta gudana a birnin Marrakech, na kasar Morocco a ranar 16 ga watan Disamba mai zuwa.
‘Yan wasan da suka samu shiga cikin jerin gwaraza 5 din sun hada da Simon Adingra (dake bugawa kasar Ivory Coast da kungiyar Brighton da Hove Albion wasa) da Serhou Gulrassy (dake bugawa kasar Guinea da kungiyar Borussia Dortmund wasa) da Achraf Hakimi (dake bugawa kasar Morocco da kungiyar PSG wasa) da Ademola Lookman (dake bugawa Najeriya da kungiyar Atalanta wasa) da Ronwen Williams (dake bugawa Afrika ta Kudu da kungiyar Mamelodi Sundowns wasa) dukkaninsu za su fafata domin lashe kyautar gwarzon dan wasan CAF ta bana.
Sauran rukuninin kyautar da aka sanar a yau sun hada da gwarzon mai tsaron raga na bana da dan wasan mafi kwazo fafatawa tsakanin kungiyoyi da gwarzon mai horar da ‘yan wasa na bana da dan wasa mafi kakantar shekaru na bana da kuma gwarzuwar tawagar kwallon kafar kasa ta bana.