Jerin gwanon ’yan Shi’a a Sakkwato shiri ne na siyasa – Wamakko
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana jerin gwanon da mabiya Shi’a suka yi a Sakkwato fadar jihar a matsayin wani yunkuri da wasu makiya jihar suka yi na hargitsa ta don kawar da zaman lafiyar da aka santa da shi.Gwamna Wamakko ya yi wadannan kalamai ne a ranar Litinin da ta gabata […]

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana jerin gwanon da mabiya Shi’a suka yi a Sakkwato fadar jihar a matsayin wani yunkuri da wasu makiya jihar suka yi na hargitsa ta don kawar da zaman lafiyar da aka santa da shi.
Gwamna Wamakko ya yi wadannan kalamai ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake jawabi ga jama’a a gidansa dake Unguwar Gawon Nama, jim kada da dawowarsa daga ziyarar aiki ta mako daya da ya kai kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ya ce, munafukan sun yi yunkuri ne don cimma wani kudirinsu na siyasa a zaben shekarar 2015. “Jerin gwanon na ranar Lahadi wata matsaya ce da aka cimma a wani taron da aka gudanar a makon jiya a birnin Abuja wanda ya samu halartar wani babban jami’in gwamnati (da ke tare da mu) da wani basarake da kuma wasu ’yan siyasa marasa kishi da ke Abuja, domin hargitsa wannan jihar,” inji
shi.
Gwamna Wamakko ya ce, a matsayinsu na shugabanni ba za su bari wasu masu muguwar manufa su karkatar da muradun al’ummar jihar ba. “Ina kara nanata kudirin da muke da shi na kare muradun al’ummar wannan jiha, irin wannan yunkuri nasu ba zai tursasa mu ga abin muka yi imani da shi ba, a matsayinmu na Musulmi Allah dai ke iya wa dan Adam wani abu, domin haka Allah kadai ke iya kawo wa Alu cikas ba wani ba,” inji Gwamnan.
Ya jinjina wa al’ummar jihar bisa dattakon da suka nuna a lokacin jerin gwanon, ya ce irin halayyar da jama’a suka nuna ya tabbatar cewa su ma’abuta son zaman lafiya ne da biyayya da doka da oda. Kuma ya bukaci su dore da haka ta yadda za su kare kyakkyawan sunan da aka san Jihar Sakkwato da shi.