Jerin jihohin da suka ba da hutun Sabuwar Shekarar Musulunci

Akalla gwamnatocin jihohin 10 a Najeriya ne suka ba da hutun shiga Sabubwar Shekarar Musulunci ta 1446 Bayan Hijira.

Jerin jihohin da suka ba da hutun Sabuwar Shekarar Musulunci

Akalla gwamnatocin jihohi 10 a Najeriya ne suka ba da hutun shiga Sabubwar Shekarar Musulunci ta 1446 Bayan Hijira.

Daga cikinsu Jihar Osun ta ba da na kwana biyu, Juma’a da Litinin, sauran kuma suka ba da na kwana guda, Litinin.

Jihohin sun bukaci al’ummar Musulminsu su dage wajen gudanar da add’u’oin neman aminci da karuwar arziki da albarka.

Jihohin ga jerin jihohin:

  1. Kano
  2. Sakkwato
  3. Katsina
  4. Borno
  5. Jigawa
  6. Yobe
  7. Bauchi
  8. Kebbi
  9. Kwara
  10. Osun
  11. Oyo

Sarkin Musulmi kuma Shugabana Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci a Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya sanar da Ranar Lahadi, 6 ga watan Yuli, 2024, a matsayin  1 ga wayan Muharram, 1446 Bayan Hijira.