Jerin jiragen alfarma 10 da Najeriya ta dakatar

Hukumar NCAA ta soke lasisin jiragen kashin kai guda 10 na yin shawagi a Najeriya

Jerin jiragen alfarma 10 da Najeriya ta dakatar

Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da wasu jiragen kashin kai guda 10 daga yin shawagi a kasar.

Ga jerin kamfanonin jiragen alfarman da NCAA ta dakatar:

  1. Azikel Dredging Nigeria Ltd
  2. Bli-Aviation Safety Services
  3. Ferry Aviation Developments Ltd
  4. Matrix Energy Ltd
  5. Marrietta Management Services Ltd
  6. Worldwide Skypaths Services
  7. Mattini Airline Services Ltd
  8. Aero Lead Ltd
  9. Sky Bird Air Ltd
  10. Ezuma Jets Ltd.

Daraktan hulda da jama’a na NCAA, Michael Achimugu, ya sanar cewa hukumar ta tura jami’ai zuwa rumfunan kamfanonin da umarnin ya shafa domin sa ido kan su.

NCAA ta soke lasisin jiragen ne saboda sun ki bin umarninta na zuwa a tantance su da kuma sabunta takardunsu.

Hukumar ta umarci jiragen kashin kai su sabunta takardu ne bayan bincike ya gano cewa wasunsu na daukar fasinjar haya domin samun kudade.

A kan haka ne ta ba umarce su su su sabunta takardu a kuma tantance kafin ranar 19 ga Afrilu, 2024.

Dokar hukumar dai ta haramta harkar hayar fasinja ko dakon kaya ko sakonni ga jiragen kashi kai a kasar.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa