Jerin shugabannin gudanarwar NNPCL 9 da Tinubu ya naɗa

Naɗin ya yi daidai da tanadin sashe na 59 (2) na dokar masana’antar man fetur ta shekarar 2021.

Jerin shugabannin gudanarwar NNPCL 9 da Tinubu ya naɗa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake naɗa Mele Kolo Kyari a matsayin shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPCL.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, mai magana da yawun Shugaban Kasar, Ajuri Ngelale, ya ce naɗin zai fara aiki daga ranar Juma’a 1 ga watan Disambar 2023.

Ana iya tuna cewa, watan Yunin 2019 ne tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara naɗa Kyari a matsayin shugaban kamfanin na NNPCL.

Shi ne ya gaji marigayi Maikanti Baru, wanda ya yi ritaya daga aiki kafin rasuwarsa.

Cikin sanarwar, Ngelale har ila yau ya ce Tinubu ya kafa kwamitin gudanarwar kamfanin wanda Cif Pius Akinyelure zai jagoranta a matsayin shugaban da ba na zartarwar ba.

Ngelale ya ce naɗin ya yi daidai da tanadin sashe na 59 (2) na dokar masana’antar man fetur ta shekarar 2021.

Sauran ’yan kwamitin sun haɗa da; Alhaji Umar Isa Ajiya da Mista Ledum Mitee da Malam Musa Tumsa da Malam Ghali Muhammad.

Ragowar sun kunshi Farfesa Mustapha Aliyu da Mista David Ogbodo da kuma Misis Eunice Thomas.