Jerin shugabannin Hezbollah da Hamas da Isra’ila ta kashe daga 7 ga Oktoban 2023
A ranar 17 ga watan Oktoba ne, Isra’ila ta sanar da kisan Yahya Sinwar, wanda shi ne ya tsara harin ranar 7 ga watan Oktoban bara da mayaƙan Hamas suka ƙaddamar kan Isra’ila da ya haifar da ɓarkewar yaƙin Isra’ila da Hamas. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ilar take ruwan bama-bomai a […]
A ranar 17 ga watan Oktoba ne, Isra’ila ta sanar da kisan Yahya Sinwar, wanda shi ne ya tsara harin ranar 7 ga watan Oktoban bara da mayaƙan Hamas suka ƙaddamar kan Isra’ila da ya haifar da ɓarkewar yaƙin Isra’ila da Hamas.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ilar take ruwan bama-bomai a Lebanon da suka yi sanadiyyar halaka manyan jagororin Ƙungiyar Hezbollah a ’yan makonnin nan, ciki har da Hassan Nasrallah.
Ya zuwa yanzu, an kashe shugabannin Hamas da Hezbollah da dama tare da wasu masu gwagwarmayar tun bayan ɓarkewar gumurzun da ake yi a halin yanzu.
Ga jerin sunayen shugabanni da kwamandojin Hamas da Hezbollah da suka rasa rayukansu a yaƙin da ake gwabzawa
- Yahya Sinwar: Shi ne shugaban Hamas a Zirin Gaza, dakarun Isra’ila sun halaka shi a wani ɗauki ba daɗi a Gaza. Ya kasance mai kaifin adawa da mamayar da Isra’ila take yi wa yankunan Falasɗinawa da kuma sadaukar da kai ga aƙidar Islama ta Hamas.
- Hassan Nasrallah: Sayyed Hassan Nasrallah na Lebanon, wanda Isra’ila ta sanar da kisan sa a ranar 28 ga Satumba, 2024, ya jagoranci Hezbollah a cikin shekarun da ƙungiyar ta yi tana fafatawa da Isra’ila. Nasrallah ya kasance wanda ya ja ragamar Hezbollah ta rikiɗe zuwa rundunar soji mai ƙarfin faɗa a ji a yankin sannan ya zama guda cikin fitattun Larabawa a shekaru da dama – tare da samun goyon bayan Iran.
- Fatah Sharif: A ranar 30 ga Satumban bana, rundunar sojin Isra’ila ta ce ta ‘kawar da’ shugaban Hamas Fatah Sharif a Lebanon, yayin da take ci gaba da kai hare-hare kan ƙungiyoyin mayaƙa masu samun goyon bayan Iran a maƙwabciyar ƙasar.
- Ali Karaki: An kashe ɗaya dagacikin manyankwamandojin ƙungiyar ta Hezbollah, Ali Karaki a harin da Isra’ilar ta kai ta sama da ya halaka Hassan Rundunar sojin Isra’ila ta ce, sama da mayaƙa 20 ne ta kashe waɗanda suka kasance masu manyan muƙamai daban-daban a ƙungiyar a yayin harin da ta kai kan wata garkuwa ko maɓuyar ƙarƙashin ƙasa.
- Nabil Kaouk: Kaouk, wanda aka halaka a harin sama ranar 28 ga watan Satumba, ya kasance mataimakin shugaban Majalisar Ƙoli ta Hezbollah.
- Mohammed Srur: Srur shi ne shugaban sashen jirage marasa matuƙa na Hezbollah, wanda aka yi amfani da shi a karon farko a wannan rikicin da ƙungiyar take fafatawa a yanzu da Isra’ila. A ƙarƙashin jagorancinsa, Hezbollah ta ƙaddamar da jirage marasa matuƙa masu tarwatsewa da leƙen asiri har zuwa ƙuryar Isra’ila, inda suka kutsa cikin na’urorin tsaronta, waɗanda suka fi mayar da hankali kan rokoki da makamai masu linzami da ƙungiyar take harba mata.
- Ibrahim Ƙubaisi: Shi ne ya kasance mai jagorantar ɓangaren makamai masu linzami na Rundunar sojin Isra’ila ta ce, Ƙubaisi shi ne ya kitsa yin garkuwa da kuma kisan wasu sojojin Isra’ila uku a kan iyakar Isra’ilar ta Arewaci a 2000, waɗanda aka mayar da gawarwakinsu a musayar fursunoni da ƙungiyar Hezbollah bayan shekaru huɗu.
- Ibrahim Aƙil: Shi ne kwamandan ayyukan Hezbollah da aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai a ranar 20 ga Satumba, inda aka shelanta ladan Dala miliyan bakwai a kansa – ga wanda ya ba da bayanin da zai kai ga kawar da shi – sakamakon harin bama-bamai guda biyu da aka kai a birnin Beirut a Oktoban 1983, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 300 a ofishin jakadancin Amurka da wasu sojin Amurka a wani barikin sojin ƙundumbalan Hukumar leƙen asirin Amurka CIA ta shafe shekaru fiye da 41 tana farautarsa.
- Ahmed Mahmud Wahbi: Ya kasance babban kwamandan da ke kula da ayyukan soji na runduna ta musamman ta Radwan har zuwa farkon shekarar 2024, an kashe shi a wani harin da Isra’ila ta kai kan wasu manyan kwamandoji a wajen birnin Beirut a ranar 20 ga Satumba, ciki har da Ibrahim Aƙil.
- Fuad Shukr: A wani hari da Isra’ila ta kai a yankunan Kudancin babban birnin ƙasar Lebanon a ranar 30 ga watan Yuli, ya kashe babban kwamandan Hezbollah Fuad Shukr. Shukr ya kasance ɗaya daga cikin manyan jami’an soja na Hezbollah tun lokacin da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka kafa ta a 1982.
- Mohammed Nasser: An kashe Mohammed Nasser a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a ranar 3 ga watan Yuli. Isra’ila ta ɗauki alhakin kai harin, inda ta ce shi ne ya jagoranci rundunar da ke da alhakin kai farmaki zuwa Isra’ila daga ƙuryar Kudu maso Yammacin Lebanon. Nasser, babban kwamanda ne a ƙungiyar Hezbollah, kuma shi ne yake jagorantar wani ɓangare na aikace-aikacen Hezbollah a kan iyaka, a cewar wasu manyan majiyoyin tsaro a Lebanon.
- Taleb Abdallah: An kashe babban kwamandan ƙungiyar ta Hezbollah Abdallah a ranar 12 ga watan Yuni a wani harin da Isra’ila ta kai mata, wanda ta ce ya kai hari kan wata cibiyar bayar da umarni a Kudancin Lebanon. Majiyoyin tsaro a Lebanon sun ce shi ne kwamandan Hezbollah na tsakiyar yankin iyakar kudanci kuma yana da matsayi ɗaya da Nasser.
- Mohammed Deif: An kashe guda cikin jagororin Hamas Mohammed Deif a wani hari ta sama da sojojin Isra’ila suka kai a ranar 1 ga Agusta. Deif ya kasance cikin jerin waɗanda Isra’ilar take farauta tun farkon
- Ismail Haniyeh: An kashe Ismail Haniyeh, wanda shi ne babban jagoran ƙungiyar Hamas a ranar 31 ga watan Yuli yayin wata ziyara da ya kai Tehran babban birnin Iran. Ya kasance shugaban Hamas tun Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce an kashe shi ne da wani makami mai cin gajeren zango.
- Saleh-Al Arouri: Wani hari da jiragen yaƙin Isra’ila suka kai a yankin Kudancin birnin Beirut na Dahiyeh ya halaka mataimakin shugaban Hamas Saleh al-Arouri a ranar 2 ga watan Janairun 2024. Arourin, shi ne kuma ya kafa rashen soji na Hamas, wato Ƙassam
- Marwan Issa: An kashe mataimakin kwamandan sojin Hamas Marwan Issa a wani harin da Isra’ila ta kai a watan Maris, in ji rundunar sojin Isra’ila. Ya kasance na gabagaba a jerin mutanen da Isra’ila take farautar su ruwa a jallo tare da Mohammed Deif da Yahya
- Naim Kassem: Shi ne mataimakin Nasrallah kuma shi ne mafi girman muƙami a ƙungiyar. Kassem ya kasance mataimakin shugaban
Hezbollah tun 1991 kuma yana daga cikin mambobin ƙungiyar da suka kafa Hezbollah. Kassem dai shi ne babban jami’in ƙungiyar da yake hirarraki da kafafen yaɗa labarai na cikin gida da na waje a kan rikicin da ƙungiyar take gwabzawa a halin yanzu. Bisa dukkan alamu dai mataimakin shugaban yana da faɗa a ji a ɓangarori dabandaban na ƙungiyar da suka shafi manyan batutuwan siyasa da na tsaro, har ma a batutuwan da suka shafi jagorancin addini da kuma ayyukan agaji ga al’ummar Musulmi ’yan Shi’a na ƙasar Lebanon.
A halin da ake ciki, shi ma Hashim Safieddine wanda ya jagoranci Majalisar Ƙoli ta Hezbollah da aka kyautata zaton zai maye gurbin Hassan Nasrallah – Isra’ilar ta halaka shi ranar Talatar nan a wani hari da ta kai wajen birnin Beirut.
Safieddine ɗan uwa ne (ba shaƙiƙi ko li’abi ba) ga marigayi shugaban Ƙungiyar Hezbullah, Hassan Nasrallah kuma ɗansa yana auren ɗiyar Janar Ƙasem Soleimani na Iran, wanda aka kashe a wani harin jiragen yaƙin Amurka a shekarar 2020.
Kamar Nasrallah, shi ma Safieddine ya shiga ƙungiyar Hezbollah tun farko-farkon kafuwarta, haka nan ma yana sanya baƙin rawani.
Waɗanda suke da sauran shan ruwa
Talal Hamieh da Abu Ali Reda su ne kawai manyan kwamandojin Hezbollah biyu da suka rage a raye waɗanda bisa dukkanin alamu, sojin Isra’ila ke neman su faɗa komarta.