Jerin sunayen ‘barayin’ gwamnati da kudin da suka sace
Tsohon Mashawacin Shugaban kasa Sambo Dasuki: Bisa binciken Hukumar EFCC da abin da ta gano kawai (wannan baya ga almundahanar Dala miliyan 2.1 na kayan yaki na soji) akwai Naira biliyan 126 a dama da Dala biliyan 1.5 da Fam miliyan 5.5 aka almubazzarantar ta hannun ofishinsa. Tsohuwar Ministar Mai, Dieziani Alison-Madukwe: A bincike daya […]

Tsohon Mashawacin Shugaban kasa Sambo Dasuki: Bisa binciken Hukumar EFCC da abin da ta gano kawai (wannan baya ga almundahanar Dala miliyan 2.1 na kayan yaki na soji) akwai Naira biliyan 126 a dama da Dala biliyan 1.5 da Fam miliyan 5.5 aka almubazzarantar ta hannun ofishinsa.
Tsohuwar Ministar Mai, Dieziani Alison-Madukwe: A bincike daya da EFCC ke yi a kanta akwai Naira biliyan 23 da ake zargin ta dallazar. Kuma tana da hannu a badakalar kwangilolin Strategic Alliance Contracts na Kamfanin NNPC da suka kai na Dala biliyan 3.
Laftana Janar Kenneth Minimah (mai ritaya): Naira biliyan 13.9 (EFCC ta kwato Naira biliyan 4.8 kudi da gidaje).
Laftana Janar Azubuike Ihejirika (mai ritaya): Naira biliyan 4.5 (EFCC ta kwato Naira miliyan 29).
Aled Badeh, tsohon Hafsan Tsaro: Naira biliyan 8 (An kwato Naira biliyan 4 kudi da gidaje).
Tsohon Shugaban Hukumar Kwastam Dikko Inde: Naira biliyan 40 (An kwato Naira biliyan 1.1 kudi da zababbun gidaje).
Iya Mashal Adesola Amosu: Naira biliyan 21.4 (An kwato Naira biliyan 2.8 kudi da gidaje 28 da motoci uku).
Tsohon Ministan Abuja Bala Mohammed: Naira biliyan 5 . Kotu ta bayar da umarnin karbe wasu kadarorinsa na wucin gadi.
Sanata Stella Oduah: Naira biliyan 9.8. Kotu ta bayar da umarnin kwace kadarorinta na wucin-gadi.
Tsohon Gwamnan Jihar Neja Babangida Aliyu: Ana zargi ya karbi Naira biliyan 1.6 daga NSA.
Sanata Jonah Jang tsohon Gwamnan Filato: Naira biliyan 12.5.
Bashir Yuguda, tsohon Minista a Ma’aikatar Kudi: Naira biliyan 1.5. An karbo Dala dubu 829 da 800.
Sanata Peter Nwaboshi: Naira biliyan 1.5
Aliyu Usman: tsohon mai tallafa wa Dasuki: Naira miliyan 512
Ahmad Idris: PA ga Dasuki: Naira biliyan 1.5
Rashidi Ladoja, tsohon Gwamnan Oyo: Naira miliyan 500
Tom Ikimi: Naira miliyan 300
Femi Fani-Kayode: Naira miliyan 866
Hassan Tukur, tsohon sakataren tsohon Shugaban kasa Jonathan: Dala miliyan 1.7
Nenadi Usman: Naira biliyan 1.5
Benedicta Iroha: Naira biliyan 1.7
Aliyu Usman Jawaz, abokin Dasuki: Naira miliyan 882
Godknows Igali: Sama da Naira biliyan 7