Jerin tallafin ambaliya da ya shiga hannun Gwamnatin Borno

Waɗanna su ne mutane da ƙungiyoyi da gwamnatoci da kuɗaɗe da kayan tallafin ambaliya da suka bayar ya shigo hannun Hukumar Agaji da Samar da Tallafin Ambaliyar Maiduguri

Jerin tallafin ambaliya da ya shiga hannun Gwamnatin Borno

Gwamnatin Borno ta fitar da jerin kuɗaɗe da kayan tallafi da suka shigo hannunta daga ɗaiɗaikun mutane da kungiyoyi da gwamnatoci.

Ta bayyana cewa akwai kuma alƙawuran da aka yi mata na irin waɗannan abubuwa domin tallafa wa mutanen da Ambaliyar Maiduguri ta shafa.

Daga cikin fitattun mutanen da suka ba da tallafin har da Alhaji Aliko Dangote da Aminu Ɗantata, Atiku Abubakar, Peter Obi, Matar Shugaban Ƙasa Oluremi Tinubu, Sanata Ali Ndume, Sanata Ali Modu Sheriff da mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara.

Sanarwar ta ce zuwa karfe 7 ma daren ranar Laraba, waɗannan su ne abubuwan tallafi ambaliyam da suka shigo hannunta ta asusun Hukumar Agaji da Samar da Tallafi da ta kafa:

Gwamnatocin Jihohi:

1. Gwamnatin Bauchi — Naira Miliyan 250.

2. Gwamnatin Kebbi — Naira Miliyan 200.

3. Gwamnatin Adamawa — Naira Miliyan 50.

4. Gwamnatin Yobe — Naira Miliyan 100.

5. Gwamnatin Kano — Naira miliyan 100.

6. Gwamnatin Gombe — Naira Miliyan 100.

7. Gwamntin Taraba — Naira Miliyan 100m.

8. Gwamnatin Katsina — Naira Miliyan 100.

 

Ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi:

1. Alhaji Aliko Dangote —Naira biliyan 2 (ga Hukumar NEMA).

2. Alhaji Aminu Dantata — Naira biliyan 1.5.

3. Atiku Abubakar — Naira miliyan 100.

4. Peter Obi — Naira miliyan N50m.

5. Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas — Naira biliyan 3.

6. Majalisar Dattawa — Naira miliyan 54.5.

7. Majalisar Wakilai — Naira miliyan 100m.

8. Jam’iyyar PDP — Naira miliyan 25.

9. Majalisar Dokokin Jihar Borno — Naira miliyan 60.

10. Sanata Ahmed Lawan — Naira Miliyan 50.

11. Hon Zainab Gimba — Naira miliyan 25.

12. Ibrahim Abba Umar — Naira miliyan 50.

13. Sumaila Satumari — Naira miliyan 20.

14. Hon Mallam Gana Kareto — Naira miliyan N10m.

15. Ƙungiyar Sanatoci ’Yan Arewa — Naira miliyan N10.

16. Sanata Barau Jibril — Naira miliyan 10.

17. Hon Moh’d Abubakar Maifata —bNaira miliyan 50.

18. Kudancin Borno — Naira miliyan 200.

19. Hon Zakariya Dikwa — Naira miliyan 10.

20. Al-Amanah Aid — Naira miliyan 1.

21. Hon Mohammed Imam — Naira miliyan 50.

22. HE Maina Ma’aji Lawan —Naira miliyan 10.

23. Sanata Ali Modu Sheriff —Naira miliyan 100.

24. Hon Dr Ali Bukar Dalori —Naira miliyan 50.

25. Sanata MT Monguno — Naira miliyan 50.

26. Sanata Kaka Shehu Lawan —Naira miliyan 50.

27. Hon Aliyu Betara — Naira miliyan 100.

28. Hon Abdulkadir Rahis — Naira miliyan 25.

29. Hon Ibrahim Abuna — Naira miliyan 25.

30. Hon Usman Zannah — Naira miliyan 10.

31. Hon Anjiniya Bukar Talb — Naira miliyan 10.

32. Hon Yerima Lawan Kareto —Naira miliyan 2.

33. Abdussalam Kachallah — Naira miliyan 100.

34. Awari Usman Alkali — Naira miliyan 20.

35. Eighteenth Engineering Company (EEC) — Naira miliyan 50.

36. Dan Nene Construction Company — Naira miliyan 30.

37. Matar Shuagaban Kasa, Oluremi Tinubu — Naira miliyan 500.

38. Dauda Kahutu (Rara Ra) —Naira miliyan 10.

39. Kananan Hukumomin Borno 27 — Naira biliyan 1.350.

40. Ƙungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE)/ (COREN) — Naira miliyan 10.

Kayan abinci da sauransu

1. Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC):

Buhu 20,000 ma shinkafa 25kg Kwali 20,000 na Makami

Jarka 10,000 na man girki

2. Kamfanin Sumal Food Group, Ibadan:

Sinƙi 50,000 na burodi

Karo 5,000 na biskit

3. Gwamnatin Jihar Nasarawa:

Tirela 2 na shinkafa

Tirela 2 na taliya

Tirela 2 na sukari

4. Janar Muhammad Buba Marwa (Rtd):

Tirela 10 na takin zamani ( a kan Naira miliyan 120)

5. Hon Aminu Jaji (HOR):

Buhu 600 na shinkafa

6. Ƙungiyar Injiniyoyi ta Najeriya Reshen Jihar Borno:

Turmi 10,000 na atamfa

7. Injiniya Usman Monguno:

Turmi 10,000 na atamfa

8. Alhaji Abdulkadir Ali (Matrix Energy):

Kayan abinci na Naira miliyan 120

9. National Agency for Great Green Wall:

Buhu 80 bags na shinkafa 25kg

Kato 30 na galan-galam ɗin man gyada.

Katon 30 ma Makaroni.

Katon 30 na taliya.

Riaho 60 masu amfani da kananzir.

Manyan tukwane girki 73.

Tabarmi 180 mats.

Kujerun roba 175.

Bokitan roba 600.

Kwanukan xin abinci 578.

Turame da taɓare 78.

Darduman Sallah 32.

100-foot mats,

Farantai 250.

Silifas 256.

Kofunan roba 700 rubber.

Kofunan Silva 353.

Robobin cin abinci 409.

Burodi 291.

Rigunan girki 192.

Tawul din goge hannu 96.

Cokula 433.

10. Hukumar Kula da Aikin Injiniya ta Najeriya (COREN):

Gwanjon tufafi masu nauyin 400kg.