Jerin ’yan daban Kano 13 da ake nema ruwa a jallo

’Yan sanda sun fitar da jerin sunayen manyan ’yan daba 13 da suke farauta a birnin Kano

Jerin ’yan daban Kano 13 da ake nema ruwa a jallo

Hedikwatar ‘yan sandan Jihar Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta bayyana sunayen wasu gaggan ’yan dana 13 da suka addabi garin Kano a baya-bayan nan.

Rundunar ta sanar da neman su ruwa a jallo sakamakon zargin hannunsu a dawowar dabanci da kwacen waya musamman a yankunan kananan hukumomin Dala Gwale da kuma Birni.

Sanarwar da kakakin rundunar, Haruna Abdullahi Kiyawa ga fitar ta umarci ’yan daban da suka kai kansu hedikwatar rundunar da ke Bompai, tun kafin su shiga hannun jami’an rundunar da ke farautar su.

Wadanda ake neman su ne:

  1. Halipa Here
  2. Sheye Injiniya
  3. Yusuf Ilu
  4. Walidi Auwalu Kapinta
  5. Tijjani Rattagu
  6. Agiri Balarabe
  7. Dan Kasuwa
  8. Dan Makare
  9. Nasuru Madadi
  10. Hali Pan Pan
  11. Jamilu Piye
  12. Saiyid Zawai da da kuma
  13. Inyasi

Kiyawa ya ce rundunar ta tura karin jami’anta sassan jihar a matsayin wani bangare na matakan ta dauka na murkushe ayyukan bata-gari da kuma tabbatar da doka da oda a Kano.

Don haka ya bukaci wadanda suka san ’yan daban da ake nema da su sanar da su cewa su kai kansu, kar su gamu da fushin rundunar.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7