Jerin ’yan Najeriya mafiya tashe a 2024

Mawaka da ’yan kwallo da attajirai da ’yan siyasa da malaman addinin Najeriya na cikin ’yan Afirka mafiya tashe a duniya a 2024.

Jerin ’yan Najeriya mafiya tashe a 2024

Najeriya

’Yan Najeriya ne mutanen da suka fi tashe a diuniya a tsakanin mutanen Nahiyar Afirka a shekarar nan ta 2024 da muke bankwana da ita.

Alkaluman da kafar kididdiga ta Statistisense ta fitar sun nuna cewa mawaka da ’yan kwallo da attajirai da ’yan siyasa da malaman addini ’yan soshiyal midiyan Najeriya na cikin ’yan Afirka mafiya tashe a 2024.

Alkaluman da ta fitar na 2024  na jerin ’yan Afirka 30 mafiya tashe a duniya a shekarar, ya nuna fiye da rabinsu ’yan Najeriya ne.

Kafar Statistisense ta yi fice wajen tattara wa fitar da alkaluma da kididdiga a fannoni daban-daban a duniya. 

Mawakin Najeriya Wizkid ne mutum mafi tashe a shekarar, a yayin da ’yan kasar guda shida suka fito a cikin mutane 10 famiya tashe, ciki har da mawaki Davido da Shugaban Kasa Bola Tinubu da hamshakin attajiri, Alhaji Aliko Dangote.

’Yan Najeriya 17 ne suka fito a jerin mutane 30 mafiya tashe a shekarar da suka hada da mawaka, ’yan siyasa, malaman addini da ’yan soshiyal midiya da ’yan wasannin motsa jiki da dai sauransu.

Ga jerin ’yan mafiya tashe a 2024 da matsayin ’yan Najeriya a cikinsu:

  1. Wizkid — Mawakin Najeriya.
  2. William Ruto — Shugaban Kasar Kenya.
  3. Davido — Mawakin Najeriya.
  4. Bola Ahmed Tinubu — Shugaban Kasar Najeriya.
  5. Aliko Dangote — Dan Kasuwan Najeriya.
  6. Raila Odinga — Dan siyasar Kenya.
  7. Bobrisky — Dan Soshiyal Midiya a Najeriya.
  8. Tyla — Mawakiyar Afira ta Kudu.
  9. Peter Obi — Dan siyasan Najeriya.
  10. Liema Pantsi — Mawakin Afirka ta Kudu.
  11. Rema — Mawakin Najeriya.
  12. Rigathi Gachagua — Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Kenya.
  13. Khosi Twala — Dan Soshiyal Midiyan Afirka ta Kudu.
  14. Uhuru Kenyatta — Tsohon Shugaban Kasar Kenya.
  15. Ademola Lookman — Dan Kwallon Najeriya.
  16. Asake — Mawakin Najeriya.
  17. Very Dark Man — Dan Soshiyal Midiyan Najeriya.
  18. Drill — Mai hoton kasar Ghana.
  19. Nyesom Wike — Ministan Abuja.
  20. Cyril Ramaphosa — Shugaban Afirkata Kudu.
  21. Reno Omokri — Dan Soshiyal Midiyan Najeriya.
  22. Rose O Konadu — Mai gabatar da shirye-shirye a Ghana.
  23. Victor Osimhen — Dan Kwallon Najeriya.
  24. Baltasar Engonga — Dan siyasa a kasar Equatorial Guinea.
  25. Sharon Ooja — Jarumar fim a Najeriya.
  26. Toyin Abraham — Furodusan fim a Najeriya.
  27. Babu Owino Paul — Dan siyasar Kenya.
  28. Chidimma Adetshina — Model a Afirka ta Kudu.
  29. Danny Walter — Dan Soshiyal  Midiya a Najeriya.
  30. Enoch Adeboye — Malamin addini a Najeriya.