Jerin zanga-zanga da suka girgiza Najeriya

Ga jerin wasu manyan zanga-zanga da aka gudanar a tsawon kimanin shekaru 50 da suka gabata, wadanda suka girgiza Najeriya

Jerin zanga-zanga da suka girgiza Najeriya

Aisha Yesufu a lokacin zanga-zangar EndSARS

Alhamis din nan dubban ’yan Najeriya za su gudanar da gagarumar zanga-zangar kwanaki 10 kan tsadar rayuwa da ta addabi al’umma a fadin kasar.

Ga jerin wasu manyan zanga-zanga da aka gudanar a tsawon kimanin shekaru 50 da suka gabata, wadanda suka girgiza kasar.

1- Ali Must Go (1978)

Ta farko ita ce zanga-zangar ALI MUST GO, wato DOLE ALI YA TAFI, a shekara ta dubu da dari tara da sabai’n da takwas, saboda gwamnatin sojin Janar Olusegun Obasanjo ta yi karin kobo 50 a kudin abincin dalibai daga Naira daya da kobo 50 zuwa Naira biyu.

Wannan karin sule biyar ya sa dalibai bore a sassan Nijeriya, irin su Legas, Kaduna, Zaria da sauransu. 

A sakamakon wannan zanga-zanga aka rasa ran mutum dalibai 8 a Jamia’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da wani daya daga Jami’ar Legas (UNILAG). 

2- SAP (1989)

Zanga-zangar SAP wadda aka gudanar a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ta girgiza Najeriya.

Dimbin daliban jami’a ne suka yi zanga-zangar sakamakon bashin da gwamnatin ta ciyo daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF)  a karkashin shirin SAP domin rage matsalar tattalin arziki.

A lokacin IMF ta sharxanta wa ƙasashe masu karbar bashin su ɓullo da wasu tsare-tsaren tattalin arziki da suka hada da cefanar da kamfanonin gwamnati, zuba jari a kasashen waje da sauransu.

An gudanar da zanga-zangar ce sakamakon illar da wadannan tsare-tsare suka yi a rayuwar ’yan Najeriya.

3- June 12 (1993)

Ta biyu ita ce Zanga-zangar JUNE 12 da aka gudanar a zamanin tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, a shekarar alif da dari tara da casa’in da uku (1993).

Zanga-zagar June 12 ta barke ne yankin Kudu maso Yamma, bayan gwamnatin Babangida ta soke zaben shugaban kasa da ake zaton cewa Cif Moshood Abiola ne ya lashe.

Mutane da dama sun rasa rayukansu a sakamakon wannan tarzoma ta June 12.

An yi wa zanga-zangar lakabi da June 12 ne, kasancewar a ranar 12 ga wayan yunin shekarar aka gudanar da zaben shugaban kasar da aka soke.

3- Occupy Nigeria (2012)

Sai ta uku, Occupy Nigeria A shekarar 2012, lokacin da gwamnatin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ta janye tallafin man fetur.

’Yan Najeriya sun fito zanga-zangar OCCUPY NIGERIA ne saboda karin farashin litar man fetur daga N75 zuwa N141 a sakamakon cire tallafin man. 

A wannan zanga-zanga, mutane sun rasa rayukansu, amma a karshe gwamnatin Jonathan ta janye karin farashin man, ta kuma dawo da tallafin.

4- Bring Back Our Girls (2014)

Na hudu; #BRINGBACKOURGIRLS; 

An yi Zanga-zangar Bring Back Our Girls ne sakamakon sace dalibai mata 276 da kungiyar Boko Haram ta yi a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno a shekarar 2014.

Zanga-zangar Bring Back Our Girls da aka fara a zamanin Jonathan ce wacce ta fi amo da kuma dadewa ana gudanarwa a Najeriya, kuma ta samu karbuwa a fadin duniya. 

Shugabannin manyan kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa sun shiga wannan gangami domin yin matsin lamba domin ganin gwamnati ta ceto daliban.

Masu gangamin BringBackOurGirls a Najeriya sun yi tattaki zuwa Majalisa Dokokin Kasar da ke Abuja, suka yi kira da a dauki mataki a ranar 30 ga watar Afrilu.

Daga bisani suka tare a Abuja, inda kullum suke gudanar da jawabai da kira domin ganin gwamnati ta kubutar da ’yan matan na Chibok.

5- Neman Karin Albashi (NLC)

Sai na biyar, zanga-zangar neman karin albashi.

A 2018 Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta jagoranci zanga-zangar namen karin mafi karancin albashi daga N18,0000 a zamanin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A karshe wannan zanga-zanga ta gama-gari ta yi nasara, inda gwamnatin ta kara mafi karancin albashin zuwa N30,000.

 

6- EndSARS (2020)

Na shida, EndSARS.

Har wa yau a shekara ta 2020 a zamanin Buhari aka kara wata zanga-zangar gama-gari, mai suna EndSARS. 

Wannan zanga-zanga wadda ta rikide ta tarzoma ta samo asali ne daga zargin cin zali da ake wa ’yan sanda a kasar.

Zanga-zangar EndSARS ya ta janyo an rasa rayuka akalla 56, wadanda  12 daga cikinsu a Jihar Legas aka kashe su.

 

7- CIRE TALLAFIN FETUR DA LANTARKI

Sai kin kara da zanga-zangar da aka yi a zamanin Tinubu domin shi ne na karshe-karshen nan da kusan kowa zai iya sani.

 

Shin a tunaninku zanga-zangar lumana na haifar da masalaha, ba tare da tarzoma ba?