Jessica Cox, wata mata ce mai abin al’ajabi domin an haife ta ne ba ta da hannaye, amma hakan bai hana ta cika burinta na zama direbar jirgin sama ba, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta bayyana. Matar mai shekara 32 da haihuwa wadda take zaune
Jessica Cod, wata mata ce mai abin al’ajabi domin an haife ta ne ba ta da hannaye, amma hakan bai hana ta cika burinta na zama direbar jirgin sama ba, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta bayyana. Matar mai shekara 32 da haihuwa wadda take zaune a Jihar Arizona da ke kasar Amurka, […]
Jessica Cod, wata mata ce mai abin al’ajabi domin an haife ta ne ba ta da hannaye, amma hakan bai hana ta cika burinta na zama direbar jirgin sama ba, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta bayyana.
Matar mai shekara 32 da haihuwa wadda take zaune a Jihar Arizona da ke kasar Amurka, ta fara amfani da hannayen roba lokacin da take yarinya kafin daga bisani ta yi watsi da su domin dogaro da kafafunta kacokan.
Lokacin da take zantawa da manema labarai ta ce, “babu wani abu da mai hannu yake yi wanda ni ma bana yi.” Har ila yau, ta bayyana cewa a shekarar 2010 ne ta zama mace mara hannu ta farko a duniya da aka bai wa lasisin tukin jirgin sama bayan ta kammala koyon tukin da kafafunta.
Bugu da kari, baya ga gudanar da aikace-aikacen yau da kullum da kanta, Cod ta iya tukin mota da kuma amfani da na’urar kwamfuta. Amma ta ce abu guda da ya rage mata ta koya shi ne gyaran gashi.
A shekarar 2012 ne dai aka daura mata aure da wani saurayinta mai suna, Patrick Chamberlain, wanda har yanzu kuma suke tare.