Jibi Arsenal za ta hadu da Chelsea

A ci gaba da gasar Firimiya ta Ingila a jibi Lahadi ake sa ran za a yi Karon-Battar Birnin Landan a tsakanin kulob din Arsenal da Chelsea. Wasan zai gudana ne a filin wasa na Arsenal da ake kira Emirates da misalin karfe uku na rana agogon Najeriya. Kamar yadda jadawalin gasar ya nuna, wannan ne […]

Jibi Arsenal za ta hadu da Chelsea

A ci gaba da gasar Firimiya ta Ingila a jibi Lahadi ake sa ran za a yi Karon-Battar Birnin Landan a tsakanin kulob din Arsenal da Chelsea.

Wasan zai gudana ne a filin wasa na Arsenal da ake kira Emirates da misalin karfe uku na rana agogon Najeriya.

Kamar yadda jadawalin gasar ya nuna, wannan ne wasa mafi zafi a wannan mako kuma shi ne wasa karo na 20 bayan da aka fara gasar.

Wannan ne wasa na biyu da sabon kocin Arsenal Mikel Arteta zai jagoranta.