Jibi Chelsea za ta kece raini da Manchester United

A cigaba da fafafatawa a gasar rukunin firimiya na Ingila, a jibi Lahadi 7 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran za a kece raini a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da kuma ta Manchester United a wasa karo na 25.  Wasan zai gudana ne da misalin karfe 7 na dare […]

Jibi Chelsea za ta kece raini da Manchester United
Jibi Chelsea za ta kece raini da Manchester United

A cigaba da fafafatawa a gasar rukunin firimiya na Ingila, a jibi Lahadi 7 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran za a kece raini a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da kuma ta Manchester United a wasa karo na 25.  Wasan zai gudana ne da misalin karfe 7 na dare agogon Najeriya.
Manchester United wacce ta farfado wajen lashe wasanni a ’yan kwanakin nan, yanzu haka ita ce ta biyar a teburin gasar da maki 40 yayin da Chelsea kuma take ta 14 da maki 28.
Idan Manchester United ta samu nasara a wasan zai karfafa mata gwiwar kasancewa daya daga cikin kungiyoyin da ke sahun gaba a teburin gasar.  Haka kuma idan Chelsea ce ta samu nasara, za ta farfado daga doguwar sumar da ta yi kasancewa tana daga cikin kungiyoyin da ke kasan tebur a gasar.
Yanzu dubban masu sha’awar kallon kwallo ne suka zuba ido su ga yadda wasan zai kaya.   Ana sa ran gtidajen nuna kallon kwallo a ciki da wajen kasar nan za su cika makil don kashe kwarwatar idanu.
Tuni magoya bayan kungiyoyin biyu a sassan duniya suka yi hasashen kulob din da suke ganin shi zai samu nasara a wasan.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa