Jibi za a bude kasuwar kayan masarufi don Ramadan a Kaduna
Hadin gwiwar wasu kungiyoyi a Kaduna ya shirya kafa wata kasuwar musamman, wadda za ta samar da kayayyakin masarufi cikin farashi mai sauki albarkacin azumin watan Ramadan da kuma shagulgulan sallah.Sakataren kungiyar Salinga Foundation, Alhaji Najib Tsafe ne ya bayyana wa Aminiya haka ranar Lahadi, inda ya ce an kammala shirye-shiryen da suka dace don […]

Hadin gwiwar wasu kungiyoyi a Kaduna ya shirya kafa wata kasuwar musamman, wadda za ta samar da kayayyakin masarufi cikin farashi mai sauki albarkacin azumin watan Ramadan da kuma shagulgulan sallah.
Sakataren kungiyar Salinga Foundation, Alhaji Najib Tsafe ne ya bayyana wa Aminiya haka ranar Lahadi, inda ya ce an kammala shirye-shiryen da suka dace don bude kasuwar, wadda za ta fara ci jibi Lahadi, a mazaunin kasuwar duniya da ke Rigachikun.
Ya ce: “kungiyarmu da kungiyar Shade da kuma kungiyar ’yan kasuwa da masu masana’antu (wato KACCIMA), ne ke jagorantar wannan aikin. Kuma mun kammala dukkannin shirin da ya dace don bude kasuwar, wanda shi ne karo na farko a tarihin Jihar Kaduna. Mun samu ’yan kasuwa manya da kanana, wadanda za su baje-kolin kayayyakin abinci da kuma na tufafi cikin rahusa. Dalilin kafa wannan kasuwa ya samo asali ne daga yadda farashin kayayyaki ke tashi da zarar watan azumi ya kawo jiki. Don magance hakan, sai muka samar da irin wannan kasuwa don sayar da kayayyakin da aka fi bukata lokacin azumi da kuma bikin sallah, bisa farashi mai sauki a kan sauran kasuwanninmu na yau da kullum.”
Ya ce suna da burin gudanar da wannan kasuwar a lokacin bukukuwan Kirsimeti, saboda su ma mabiya addinin Kirista su amfana da wannan garabasar.
Ya ce za a yi amfani da kudin shigar da aka samu daga kasuwar don gudanar da ayyukan taimakon jama’a, kamar marayu da sauran mabukata.