Jibi za a hadu tsakanin Chelsea da Man United, Manchester City kuma da Arsenal
A Jibi Lahadi ne idan Allah Ya kaimu za a yi wasanni masu zafi a Gasar rukunin firimiyar Ingila ta bana. Kamar yadda jadawalin Gasar ta nuna, kulob din Manchester City ne zai fara haduwa da na Arsenal da misalin karfe 3 da kwata na rana agogon Najeriya. Za a yi wasan ne a filin […]

A Jibi Lahadi ne idan Allah Ya kaimu za a yi wasanni masu zafi a Gasar rukunin firimiyar Ingila ta bana.
Kamar yadda jadawalin Gasar ta nuna, kulob din Manchester City ne zai fara haduwa da na Arsenal da misalin karfe 3 da kwata na rana agogon Najeriya. Za a yi wasan ne a filin wasa na Etihad na Manchester City.
Kawo yanzu Manchester City ce take jan ragamar teburin gasar da maki 28 daga wasanni 10 yayin da kulob din Arsenal yake matsayi na 5 da maki 19.
Da misalin karfe 5 da rabi na yammacin ranar ce kuma za a yi wasa a tsakanin kulob din Chelsea da na Manchester United. Shi ma wasa ne da zai yi zafi don dukkan kungiyoyin biyu suna neman samun nasara ne a wasan. Yayin da Manchester United take matsayin na biyu a teburin gasar bayan ta hada maki 23 ita kuwa Chelsea tana matsayi na 4 ne da maki 19.
Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil da magoya baya don ganin yadda wasannin za su kaya.