Jibi za a shawo ta tsakanin Liberpool da Tottenham
A ci gaba da fafatawa a gasar rukunin-rukuni na Firimiya na Ingila a jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Liberpool da na Totenham. Za a yi wasan ne da misalin karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Liberpool wato Anfield. Wasan […]
Liberpool VS Tottenham
A ci gaba da fafatawa a gasar rukunin-rukuni na Firimiya na Ingila a jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Liberpool da na Totenham. Za a yi wasan ne da misalin karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Liberpool wato Anfield.
Wasan shi ne na 32 bayan da aka fara gasar ta bana. Kawo yanzu Liberpool ce take saman teburin da gasar bayan ta hada maki 76 a wasanni 31. Sai Manchester City ke biye da maki 74 amma tana da kwantan wasa daya, sai kuma kulob din Tottenham a matsayi na uku da maki 61, yayin da Arsenal ke matsayi na hudu da maki 60 kuma sai kulob din Manchester United a matsayin na biyar da maki 58.
Ke nan, wasan na jibi zai gudana ne a tsakanin kungiyar da ke matsayi na 1 wato Liberpool da wadda ke matsayi na uku wato Tottenham.
Masana harkar kwallo sun yi hasashen za a yi gumurzu sosai ganin kulob din Liberpool yana kokarin kofin Firimiya na Ingila a bana a karon farko bayan shekaru fiye da 20, yayin da Tottenham ba za ta bari a yi mata sakiyar da ba ruwa ba, ganin kulob din Arsenal na biye da ita a-gindi-a-gindi.
Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika don ganin yadda wasan zai kaya.