Jibi za a yi gumurzu a tsakanin FC Barcelona da Real Madrid
A jibi Lahadi ake sa ran za a yi gumurzu a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na FC Barcelona da kuma na Real Madrid a gasar rukunin La-Liga na Sifen. Za a yi wasan ne a filin wasa na Nou Camp da ke Barcelona da misalin karfe 9 na daare agogon Najeriya. Wasan shi ne wasa […]
A jibi Lahadi ake sa ran za a yi gumurzu a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na FC Barcelona da kuma na Real Madrid a gasar rukunin La-Liga na Sifen. Za a yi wasan ne a filin wasa na Nou Camp da ke Barcelona da misalin karfe 9 na daare agogon Najeriya.
Wasan shi ne wasa mafi zafi a duk fadin duniya, don wadansu ma sukan ce duniya takan tsaya cik ne a duk lokacin da kungiyoyin biyu suke wasa saboda zafinsa da kuma armashi.
Idan kulob din FC Barcelona ya kuskura ya bari na Real Madrid ya doke shi, to na Madrid din ne zai koma sama a teburin gasar ta La-Liga da maki biyu yayin da idan Barcelona ce kuma ta samu nasara a wasan, to ko shakka babu za ta cigaba da rike ragamar gasar da maki 4.
A wasannin da kungiyoyin biyu suka hadu a watan Oktobar bara, Real ce ta samu nasara da ci 3-1.
Ana sa ran kimanin ’yan kwallo fiye da miliyan 100 ne za su kalli yadda wasan zai kaya a akwatunan talbijin a sassan duniya.
A halin yanzu FC Barcelona ce take samun teburin gasar da maki 65 a wasanni 27 yayin da Real Madrid ke biye da ita da maki 64 daga wasanni 27.