JIBWIS ta tara miliyan 100 daga fatun layyar da aka ba ta — Sheikh Bala Lau
Za a yi amfani da kudin ne a ginin jami’ar da kungiyar take yi
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), ta ce ta tara kusan Naira miliyan 100 bayan sayar da fatun ragunan da aka tattara mata a Sallar Layyar da ta gabata.
Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya sanar da haka a Abuja ranar Asabar.
- Tikitin Musulmi da Musulmi ya gwara kan Tinubu da Atiku
- An gano gawar mutum 26 da suka nutse a ruwa a kokarin tsere wa ’yan bindiga
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi yayin bikin yaye dalibai mahaddata Alkur’ani a makarantar kungiyar da ke Abuja.
Ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen aikin gina Jami’ar Salam da kungiyar take yi garin Hadejia na jihar Jigawa.
Shugaban ya kuma taya daliban da suka haddace Alkur’anin yayin saukar da suka hada da mata 22 da maza tara murna.
Sheikh Bala Lau ya kuma bukace su da su yi amfani da abin da suka karanta, inda ya ce kamata ya yi a ga karatun a mu’amalarsu ta yau da kullum.
Ya kuma ce makarantar ta sami tallafin Naira miliyan biyar daga daya daga cikin iyayen daliban da suka yi saukar, wanda ya nemi a sakaya sunansa.