JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (10)
Tun da ta gama wanka kimanin minti talatin ke nan, Saratu tana zaune gaban dogon madubi, tana ta fesa kwalliya. Shafa wannan hoda, zizara wannan janbaki, dosana wannan jagira, ko gajiya ba ta yi. Idan dai batun kwalliya ne, ba ta wasa da ita. Idan har akwai dalilin da za ta yi kwalliya, to takan […]
Tun da ta gama wanka kimanin minti talatin ke nan, Saratu tana zaune gaban dogon madubi, tana ta fesa kwalliya. Shafa wannan hoda, zizara wannan janbaki, dosana wannan jagira, ko gajiya ba ta yi. Idan dai batun kwalliya ne, ba ta wasa da ita. Idan har akwai dalilin da za ta yi kwalliya, to takan iya shafe awa daya ko ma fiye da haka, har sai ta samu gamsuwa cewa ta gama cakarewa.
Yau kwana uku ke nan da Binta ta gayyace ta bikin ranar hauhuwarta. A yau Asabar za a yi bikin, wanda ake sa ran farawa da misalin karfe hudu da rabi na maraice. Tuni Saratu ta gayyaci Alhaji Baba, wanda shi kuma ya sha alwashin halarta. Hasali ma, shi zai zo da motarsa ya dauke su, ita da kawar tata.
Tana tsakar kwalliya, sai ga Binta ta shigo gidan nasu, tare da sallama. Bayan ta gaishe da mahaifiyar Saratu, ta yi wa dakinta tsinke. Tun daga nesa ta jiwo muryar mawaki Nura M. Inuwa tana tashi. Koda ta je bakin kofa ta fara sallama, amma babu wanda ya amsa, domin kuwa Saratu ta shagaltu da kwalliya, a yayin da take bin wakar Nura sau da kafa, kamar ita ce ta rera ta.
***
“Na samu wacce nake so,
Ta dauraye ni da soso,
Ba mai kira na da kwafso,
Za nai kalamin bakina kan wacce rai ke kauna.”
Saratu ce ta gantsare a bakin madubi, tana rawa da kai, a yayin da take rera wannan baiti. Sai dai kawai ta ji an kawo mata rida ta baya.
Ta yi farat, ta mike tsaye, tare da juyowa baya cikin mamaki. “Haba Bintoto! Ke ce kika razana ni haka?”
“To, yaya kike so da ni? Na yi sallama har na gaji, ke kuwa kina nan kina ta shan wakar soyayya.” Binta ta fadi haka, a yayin da ta rika kallon kwalliyar kawarta.
“Iyeee! Lallai yarinyar nan kin fito, sai ka ce wata amarya!”
“Kin ji ki, to me ya raba dambe da fada?” Saratu ta fadi haka, yayin da ta karkace tana rangajin rawa, tana bibiyar baitukan wakar Nura M. Inuwa.
“In ka ga so yai tsada,
Da ma ciki ba yarda,
Wannan alamar shaida,
Tushe na so raunin zuci harshe kalami kauna.”
Binta ta yi kasake tana kallonta cikin mamaki. “To wai ke wannan rawar ta mece ce?”
Saratu ta yi banza da ita, ta ci gaba da rausayawa, tare da bibiyar baitukan wakar.
“Ga shawara ga masoya,
So mai kamar angurya,
In za ka fara shriya,
Buri na rai sigar kauna in samu mai kishina.”
Saratu ta yi wata zarya cikin gwanancewar rawa, ta matso kusa da kawarta, ta nuna ta da hannu, ta ci gaba da bibiyar wannan baitin na gaba:
“Sa’a ko nayyo dace,
Na samu yarinya ce,
Ba ta da tsiwar zance,
Duk bincikena ya nuna min ba ta aikin barna.
*
“Cikin sonta na nitsa kaina,
Tana nuna tausai guna,
Ashe dole ta shiga raina,
Domin zuciya duk mai sonta ta so shi zancen kauna.
*
“Buda shafuka ka karanta,
Tana sona na rike sonta,
Hanya sun raba da kazanta
Samunta mazaunin matata shi ne cikar burina.
*
“Mai dan gwargwadon siffa ce,
Fara mai tsayi a takaice,
Zubin ’yar Fulani kamance,
Mai hanci idanu ga gashi baki ga ta mai kyan suna.
*
“Cikin ranta ba ta da kyashi,
Kullum gaskiya taka feshi,
Suna nata ban kama shi,
Don nuna mai yin saurare kyawun rufe sirrina.
*
“Hatta ita ma da kawaye,
Ba ta bibiyar sawaye,
Ta more cikin sunaye,
Ba ta gulma bare karya su ne irin tsarina.”
Tana gama wannan baitin, sai ta rugo da gudu ta fada kan Binta, wacce ke zaune a kushin tana kallon ikon Allah. Suka bushe da dariya. Ko kafin su natsa, yaro ya zo daga kofar gida, ya sanar da su cewa ana sallama da Saratu a kofar gida.
“Kin ji gwanina, dan halas har ya zo,” inji Saratu. “Dalin nawa ne ya zo, dama ya ce tun wajen karfe uku zai zo. Shi ya sanya ma kika ga na kammala kwalliyata tun dazu.”
“Ai ni wannan zakwadin naki har ma kin fi mai kora shafawa. Biki nawa amma kin ma fi ni murna.”
“Akwai dalili mai girma da ya sa nake murna. Kaunar mutumin nan ce take kara murkushe ni.” Saratu ta fadi haka, a yayin da ta figi hijabi ta rufa wa kanta, ta yi waje cikin sauri. Ta bar kawarta cikin mamaki.