JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (15)

A ci gaba da wannan labari, mun tsaya ne daidai inda aka ce: Farida ta rasa abin da za ta yi, ta fashe da kuka. A cikin kukan ne take magana. “Wannan takaici da me ya yi kama?” A cikin daren nan ta bude kofa ta fita waje, daga ita sai suturar jikinta. ’Ya’yanta suka […]

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (15)

A ci gaba da wannan labari, mun tsaya ne daidai inda aka ce: Farida ta rasa abin da za ta yi, ta fashe da kuka. A cikin kukan ne take magana. “Wannan takaici da me ya yi kama?”

A cikin daren nan ta bude kofa ta fita waje, daga ita sai suturar jikinta. ’Ya’yanta suka bi bayanta suna cewa ta dawo gida amma ba ta saurare su ba. Sai da gari ya waye ne Baba ya samu tabbacin cewa yaji ta yi. Ba gidansu ta tafi ba, gidan yayarsa Tabarno ta kwana. Ga ci gaba:

Koda gari ya waye, Alhaji Baba bai farka daga barci ba sai wajen karfe goma. Ko Sallar Asuba bai samu ba sai a lokacin nan ya yi saurin gabatar da ita, bayan ya yi alwala. Ba da gangan ya makara ba, domin kuwa shi da kansa bai samu runtsawa ba sai wajen karfe hudu na asuba. Takaicin abin da ya faru tsakaninsa da Uwargida Farida shi ne ya hana shi runtsawa tsawon daren nan, domin kuwa barcin ma sace shi ya yi ba da saninsa ba.

Koda ya gama Sallah, bai koma kan komai ba sai batun matarsa Farida. Tun jiya da tsakar daren nan ya samu tabbacin cewa matarsa tana gidan yayarsa. Dalili ke nan ya dan samu natsuwa har barcin ya kama shi. Kai-tsaye ya fita daga gida, ya tunkari gidan abokinsa Mamman Tela. Ya yi kokarin samunsa tun kafin ya fita zuwa wajen aiki, domin kuwa ba ya son ya je gidan yayar tasa shi kadai.

Ya kuwa yi sa’ar samunsa a gida, yana shirin fita wajen aiki. Bayan ya shaida masa dalla-dallan abin da ya kawo shi da safe haka, ba su bata lokaci ba sai kawai suka yi wa gidan Yaya Asma’u tsinke. Yayar tasa tana zaune ne a Tarauni.

“Malam, ka san kuwa wankin hula yana neman kai ni dare? Farida ta kekashe idanunta, matsala kawai take jaza mini. Abin nan kuma ya fara ba ni tsoro, domin jiya da ta fita cikin dare, idan akwai tsautsayi wani abu na iya samun lafiyarta.” Baba yana tuka mota kuma yana yi wa abokinsa bayani.

“Abin mamaki shi ne, shin ta ina ta samu bidiyon bikin nan?” Mamman ya tambaya.

“Wallahi ni kaina abin ya daure mini kai. Na rasa ma ta inda zan biyo mata in fahimta. Shin ita ce ta sulale zuwa wajen bikin nan ko kuwa wata ce ta dauka ta kai mata?” Baba yana magana yana yake, hankalinsa a kan hanya.

“To, idan ita ce ta je wajen bikin da kanta, yaya aka yi ta riga ka zuwa gida?”

“Wannan ita ce tambayar da ba zan iya ba ka amsarta ba, domin ni kaina ina mamakin yadda aka yi wai kafin ma in dawo na iske ta da bidiyon bikin a wayarta.”

Haka suka yi ta tattaunawa har suka iso gidan Yaya Asma’u, inda bayan Alhaji Baba ya girke motarsa a kofar gidan, tare da sallama suka shiga gidan. Sun samu wuri a falo suka zauna, a yayin da Yaya Asma’u ta same su suka gaisa. Kafin su ci gaba, aka kawo musu koko da kosai. Shi dai Mamman ya ce ya riga ya karya, don haka Baba ne kawai ya take cikinsa, sannan hankalinsa ya fara dawowa.

Koda Yaya Asma’u ta zauna a kujera tana fuskantar bakinta, bayan sun sake gaisawa sai ta fara kiran sunan Mamman, ta kalubalance shi game da kanenta.

“Mai babban suna, ko ka san cewa abokinka ya zama tsuntsun da ya kira ruwan dafa kansa?” Abin da ta fada ke nan, yayin da shi kuma kanenta ya yi kasake, ya kasa cewa komai. Mamman ne ma ya samu karsashin furta wani abu.

“Yaya, wannan al’amari na Baba ina sane da shi, kodayake ban san da faruwar al’amarin jiya ba sai yau da safe da ya zo gidana.” Mamman ya fara magana, sannan ya ci gaba da cewa: “Amma ina son mu bi abin nan cikin tsanaki, insha Allah za a shawo kansa. Ba wani abu ne ke damun Farida ba illa kishi.”

“Har ka dauki matsaya ke nan tun yanzu? Wato ka goya wa abokinka baya tun kafin a je ko’ina?” Abin da ta fada ke nan, inda kafin ma ya samu mayar mata da batu sai Baba ya fara magana.

“Gaskiya Yaya, kishi ne kadai yake damunta, domin dai karin aure ba haramun ba ne.”

“To kuma wane ne ya gaya maka cewa karin aure haramun ne? Ina son ka saurari matarka da basira, akwai abin da take gani, wanda kai ba za ka gani ba, saboda shaukin soyayya ya rufe maka ido.”

Ba ta bari wani daga cikinsu ya sake magana ba, sai ta ci gaba. “Shin ka yi bincike game da yarinyar da kake shirin aure? Ka san ko ita wace ce, yaya tarbiyyarta take, yaya iyayenta suke? Shin wannan hakikicewa da kake yi wajen bibiyarta zuwa wajen bukukuwa, kana nufin aikin kirki ne kake shukawa?”

Alhaji Baba ya yi kasake yana kallon yadda yayarsa ke ta yi masa jerangiya da tambayoyi. Shi kuwa abokinsa sai kai-komo yake da idanunsa daga kan abokinsa zuwa ga yayarsa. Wannan ya nuna musu cewa matar dai tana goyon bayan Farida.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos