JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (19)

A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Madalla, ga ni nan zuwa.” Saratu ta nisa, sannan ta kashe wayar. Ba ta bata lokaci ba ta shirya ta fita daga gidansu, ta yi wa gidan su Binta tsinke. Ga ci gaba: Saratu ba ta bata lokaci ba, […]

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (19)

A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Madalla, ga ni nan zuwa.” Saratu ta nisa, sannan ta kashe wayar. Ba ta bata lokaci ba ta shirya ta fita daga gidansu, ta yi wa gidan su Binta tsinke.

Ga ci gaba:

Saratu ba ta bata lokaci ba, koda ta gama shiryawa sai ta shuri takalmanta ta bar gida. Babu inda ta yi tsinke sai gidan su kawarta Binta. Da ma tun da farko ta buga mata waya. Sai dai kafin ta isa wajen Binta, wani al’amari ya kawo mata tsaiko.

Motar A Daidaita Sahu da ta hau, ta gamu da matsala, domin kuwa suna tsakar tafiya sai wata mata wacce Saratu ta samu a motar ta samu sabani tsakaninta da direban. Lokacin da matar ta zo daidai inda za ta sauka, ta mika wa direba Naira dari biyar, shi kuma ya kirga canji ya mika mata.

“Malam, canja mani wannan Naira darin, ba ta da kyau.” Abin da matar ta fada ke nan, bayan ta murtuke fuska kamar hadari.

“Me ya samu wannan kudin? Ni ma fa ba ni aka yi, ba ni na kera ta ba,” inji direban A daidaita Sahu; shi ma ya mayar mata da bakar magana.

“Ni dai na gaya maka ba zan karbi wannan ba kuma idan kudina ne, hakkina, dole a canja mani.”

Wasa-wasa dai magana ta girma, nan suka yi ta cakusawa, wani mutum da ke cikin motar ya sanya baki, domin sasanci amma ya kasa sasanta su. Saratu da ta ga abin zai bata mata lokaci sai ta nemi fita daga motar.

“Malam, ni fa sauri nake, ina da uzuri, idan ba za mu tafi ba, zan sauka daga motar nan in kama gabana.” Abin da ta fadi wa direban ke nan, amma ko kallon wajenta bai yi ba; domin kuwa ga alama hankalinsa na kan matar nan mai canji. Shi ya yi tsayin daka cewa ba zai canja mata Naira darin ba, ita kuma ta tubure cewa akan tilas sai ya canja mata.

Cikin fushi Saratau ta sauko daga motar, ta kama hanya kawai ta bar wajen. Daga bisani sai ta tsaya ta shiga wata motar, wacce ta kai ta unguwar su Binta, kawarta.

Koda ta shiga gidan, ta iske kawar tata tana ta jiranta. “Amma gaskiya kin yi sa’a, domin minti biyar na diba, cewa idan ba ki zo ba zan kama gabana. Wani al’amari ne ni ma ya taso mani. Ke da kika ce mani ba za ki dade ba za ki iso, amma kika shanya ni haka…”

“Don Allah ki yi hakuri, ni ma ba haka na so ba. Wallahi mota biyu na shiga kafin in iso nan, matsala muka samu.” Saratu ta tarbi numfashin kawarta. “Mu samu wuri mu zauna, gaskiya bayanan nan suna da matukar muhimmanci.”

A falon mahaifiyar Binta suka zauna kan kujerin kushin. Sun yi dace, yaran gidan duk sun tafi makarantar Islamiyya, don haka babu wanda zai kawo masu matsala a yayin tattaunawarsu.

“Kawata, ina cikin manja fa!” Saratu ta fadi haka cikin yanayin takaici.

“To, fa! Wane irin manja haka babu dadin ji?” Binta ta fadi haka, a yayin da ta mike tsaye da nufin kawo wa kawarta abinci.

“Yau ina kuma za ki haka?”

“Dambu ne zan kawo maki. Tun dazu da na ji kin ce ga ki nan tafe, shi ne na ajiye maki shi. Na san ki mutunniyata, kina da son dambu.”

“Wallahi da ma kin yi zamanki mun karkare batun nan nawa, domin ko kin kawo shi ba ni da zarafin zura shi a cikina.”

Binta ba ta ma tsaya saurarenta ba, ta nufi kicin kai tsaye. Ba ta jima ba ta dawo dauke da rufaffen kwanon abinci tare da dogon, rufaffen kofin ruwa a daya hannun.

a kebe zuwa ga masoyiyata, wadda halinta daya da na Uwargida Farida sarautar mata.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos