JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (20)
A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Binta ba ta ma tsaya saurarenta ba, ta nufi kicin kai tsaye. Ba ta jima ba ta dawo dauke da rufaffen kwanon abinci tare da dogon, rufaffen kofin ruwa a daya hannun.” Ga ci gaba: Kawayen biyu sun natsu, […]
A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Binta ba ta ma tsaya saurarenta ba, ta nufi kicin kai tsaye. Ba ta jima ba ta dawo dauke da rufaffen kwanon abinci tare da dogon, rufaffen kofin ruwa a daya hannun.” Ga ci gaba:
Kawayen biyu sun natsu, sun fuskanci juna domin tattauna al’amarin da ke damun Saratu. Ko kafin su fara cewa komai, Binta ta ankara da yadda yanayin kawarta ya canja gaba daya. Duk wanda ya kalli fuskarta, ba tare da raba daya biyu ba zai fahimci cewa lallai tana cikin damuwa.
“Kawata, ki kwantar da hankalinki, ki cire damuwa daga ranki, kada ki je ki saka wa kanki wata lalura;” inji Binta, a yayin da ta ga Saratu ta buga wani uban tagumi. “Ita rayuwar nan fa ’yar taka-tsantsan ce. Kada ki ce za ki saka namiji a ranki da zurfi, domin kuwa maza ba su da tabbas.”
“Gaskiya ni na ma rasa abin da ke damuna, domin kuwa ba al’amari daya ne a cikin raina ba.” Saratu ta fara magana, a lokacin da ta kura wa kawarta ido. “Kamar yadda na gaya miki a jiya, a rayuwata yanzu, al’amura biyu ne ke saraftu a zuciyata, su ne kuma suke hana ni sukuni. Ko barci nake, idan mafarki zan yi, to dayan biyun al’amuran nan ne kan bijiro mini.”
“Ina saurarenki, ki bayyana mini su, mu ga yadda za mu bullo musu.”
“Abu na farko da ke dugunzuma mini rayuwa shi ne dangantakata da Malam Dandauda. Idan ba ki mance ba, na shaida miki yadda tu da farko muka shaku da juna. Allah na gani, na saka shi a raina kamar me, amma shi kuma ba aure ke gabansa ba.” Saratu ta tsaya da magana, a yayin da hawaye ya tsatso daga idanunta. Ta sanya hannu ta share, amma wani ya sake gudanowa.
“Ki yi hakuri, don Allah ki daina zubar da hawayenki haka.”
“Wallahi idan na tuno da abin da Dandauda ya yi mini, ji nake kamar ma in kashe kaina in huta.” Ta ci gaba da shesshekar kuka, a yayin da Binta ta ci gaba da lallashinta.
“Mutumin nan ya saka ni cikin matsala. Lokacin da ya nuna yana sona, na bukaci ya fada mini gaskiya idan ya shirya aure, amma ya yi ta yaudarata har sai da…” Ta kara kecewa da kuka har sai da ta fara ruri. Kawarta ce ma ta tallabe mata kai, ta rika share mata hawayen tare da jijjiga ta. A haka ta dan samu natsuwa, inda ta samu karsashin ci gaba da bayyana mata labarin nata.
“Mutumin nan, shi ne ya kawar mini da budurcina. Kafin in san shi, babu wani da namiji da ya taba ko kama hannuna. Kin san kuma yadda aikin Shaidan yake, idan ya kama ka, to idan ba ka yi ba, sai ka ji kamar ba ka da lafiya. Sannu a hankali har muka saba da shi, muka zama kamar miji da mata, alhali babu wanda ya daura mana aure kuma babu inda ya biya sadaki.” Ya zuwa yanzu Saratu ta daina kukan, ta fuskanci Binta, tana ta zayyana mata labarinta.
“Na yi iyaka kokarina cewa ya aika manyansa zuwa gidanmu domin maganar aure, amma mutumin nan ya yi kemudugus. Kin san wani abu?”
“Ina jin ki, sai kin fada.”
“Ko kin san a halin yanzu ciki ne da ni, wata biyu?”
“Subhanallahi! Ta yaya kika banzatar da kanki haka?” Binta ta wangale baki, ta kura wa kawarta ido cikin mamaki da kaduwa.
Za mu ci gaba