JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (8)
Koda Alhaji Baba ya kama hanyar gida, al’amura biyu ne suka mamaye zuciyarsa. Tunanin da ya rika karakaina a zuciyarsa game da soyayyarsa ne da Saratu, musamman ma farin cikin da yake tunanin zai samu idan ya aure ta. A bangare daya kuma yana tunanin abin da zai je ya zo daga bangaren matarsa, musamman […]
Koda Alhaji Baba ya kama hanyar gida, al’amura biyu ne suka mamaye zuciyarsa. Tunanin da ya rika karakaina a zuciyarsa game da soyayyarsa ne da Saratu, musamman ma farin cikin da yake tunanin zai samu idan ya aure ta. A bangare daya kuma yana tunanin abin da zai je ya zo daga bangaren matarsa, musamman ma tashin hankalin da ya ga ta shiga dangane da lamarin.
‘Yarinyar nan gaskiya tana da hankali, ga shi kuma ta iya magana da tsara kalaman barkwanci.’ Tunanin da yake yi ke nan a zuciyarsa, a lokacin da ya sha wata kwana, ya canja giya sannan ya dauki hanya dodar.
A tunanin zuci, ya yi la’akari da cewa Allah Ya hore masa matsakaiciyar dukiya, yana da sana’a mai ba shi rufin asiri. “Gaskiya bai kamata a ce ina zaune da mace daya ba. Ya zama dole ne in kara aure. Hatta Malam Kasimu, limamin masallacinmu, da na tambaye shi batun kara aure, goyon baya ya ba ni.” Ya sake tunano yadda suka yi da Liman, a lokacin da ya tuntube shi da batun kara aure.
“Ai babu abin da ya fi dadi a rayuwar dan Adam kamar zuri’a,” inji Liman. “Manzon Allah (saw) ya umurce mu da mu yi aure kuma mu hayayyafa, domin ya yi alfahari da yawan nan namu a ranar tashin alkiyama. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ba wai auren kadai za mu yi ba da nufin jin dadin saduwa da iyalinmu. Mu sani, aure ibada ne, yana da ka’idoji da sharudda da rukunoni kamar kowace irin ibada. Ya zama wajibi mu nemi iliminsa kafin mu fada cikinsa.”
Alhaji Baba ya tuno sarai da wadannan bayanai da Liman ya yi masa, har ma ya ci gaba da bayyana masa yadda ya kamata magidanci ya yi adalci tsakanin iyalansa. “Idan ka san ba za ka yi adalci ba tsakanin matanka, kada ka sake ka kara aure. “A ranar lahira, mutumin da ya ki tsaida adalci tsakanin matansa, zai tashi a shagide, bangaren jikinsa a shanye. Wannan shi ne sakamakon mai cin amana a aure ko kuma mai fifita wata daga cikin matansa na aure a duniya.” Abin da ya fada masa ke nan kuma wannan batu shi ne yake ta karakaina a zuciyarsa a yanzu.
‘To amma ni me zai hana ni yin adalci tsakanin Saratu da uwargidata Farida?’ Abin da ya fada ke nan a zuciyarsa, sannan ya ci gaba da yi wa kansa tambihi. ‘Na farko dai ina son uwargida Farida, ita ma tana so na. Auren soyayya muka yi kuma Allah Ya ba mu zuri’a daidai gwargwado, ga kuma fahimtar juna. Haka ita ma wannan yarinya, Saratu; duk da cewa ba mu dade da haduwa da juna ba, amma dai masu iya magana sun ce Jumu’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta. Ni dai kam na fahimta da cewa Saratu za ta zama matar aure tagari. Ga ilimi na addini da na zamani, ga siffar jiki mai kyau, ga…’
Zaren tunaninsa ya tsinke ne a daidai lokacin da ya taka burkin motarsa kai tsaye. Bai ankara ba sai ya ga wani yaro ya sako kekensa bisa titi a sukwane. Allah Ya taimaka ya taka burki ya tsaya cik. Dalili ke nan da yaron ya wuce da gudu, ya tsallake hanyar. Shi kuwa ya buga wata doguwar ajiyar zuciya. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!” Abin da ya fada ke nan, sannan ya ci gaba da tafiya.
***
Koda ya isa gida, sai ya iske wani sabon abin damuwa. Matarsa Farida ya iske cikin damuwa, fuskarta a turbune babu annuri kamar yadda take a baya. “Assalamu alaikum!” Ya yi mata sallama, amma shiru ba ta ce masa uffan ba. Ya dai ankara da yadda ta kura wa kofar daki ido kamar mai karatun allon bango.
“Me ke faruwa ne FATA? Kodai wani abu ya faru, ai akalla ya kamata ki amsa mani sallamar da na yi maki.” Ya fadi haka, a yayin da ya rusuna kusa da ita. A lokacin ne ma ya fahimta da cewa ko wanka ba ta yi ba saboda yadda ya ji warin zufar jikinta ya cika masa hanci. ‘Lallai kam babu lafiya, domin abin da zai hana uwargidata tsafta ba karamin al’amari ba ne.’ Tsokacin da ya yi ke nan a zuciyarsa, daga bisani kuma ya shiga dakinsa, ya bar ta a nan zaune yadda ya iske ta tun da farko.
Koda ya shiga dakinsa, Alhaji Baba bai samu sukuni ba, domin kuwa tunanin yadda zai warware wannan matsala ce ya gallabe shi. Wannan shi ne gaba kura baya sayaki. Kowane al’amari na rayuwa yana da kalubale, babu shakka al’amarin iyali shi ma na da nasa kalubalen, musamman ma batun kara aure.
Ya tunano irin shawarar da abokinsa ya ba shi, cewa kada ya sake ya bude dukkan cikinsa ga Farida, dangane da wannan aure da zai yi. A gefe daya kuma, ga shi tana da tsananin bukatar jin abin da yake ciki. Hasali ma, ya yi mata alkawarin cewa zai sanar da ita duk abin da yake ciki. To ina mafita cikin wannan daurin gwarmai da ya same shi?
Za mu ci gaba