Jiga-jigan APC sun nuna wa Tambuwal karimci wajen nada shi Matawallen Sakkwato

A ranar Asabar da ta gabata ne Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya nada Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwa a matsayin Matawallen Sakkwato, inda jiga-jigan Jam’iyyar APC suka nuna masa karimci.A wurin bikin Aminiya ta ji rade-radin cewa Shugaban Majalisar zai koma APC kafin zaben fitar da gwani na jam’iyar da […]

Jiga-jigan APC sun nuna wa Tambuwal karimci wajen nada shi Matawallen Sakkwato
Jiga-jigan APC sun nuna wa Tambuwal karimci wajen nada shi Matawallen Sakkwato

A ranar Asabar da ta gabata ne Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya nada Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwa a matsayin Matawallen Sakkwato, inda jiga-jigan Jam’iyyar APC suka nuna masa karimci.
A wurin bikin Aminiya ta ji rade-radin cewa Shugaban Majalisar zai koma APC kafin zaben fitar da gwani na jam’iyar da za a yi bayan Babbar Sallah.
Wani na hannun damarsa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Wannan shi ne bikin karshe da jagoransa ya yi kafin bikin komawarsa Jam’iyyar APC. Kuma duk wani shiri na takarar kujerar Gwamnan Jihar Sakkwato ya yi a wannan jam’iyyar.”
A jawabin Sarkin Musulmi wajen bikin ya ce, Majalisar Sarkin Musulmi ta yanke shawarar bayar da wannan sarauta ga Aminu Tambuwal ne saboda gamsuwa da yanayin jagorancinsa, don haka ya nemi Matawallen ya zama jakada nagari ga majalisar. “Mun sani dari bisa dari yana yi mana biyayya,” inji Sarkin Musulmin.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi azumin Arafa kuma su yi wa kasa addu’a a ranar kan Allah Ya kare ta daga kowace masifu, kuma Ya sa a yi zaben 2015 lafiya.
A jawabinsa na godiya Matawalle Tambuwal, y aba Sarkin Musulmi tabbacin ba zai ba shi kunya ba.  “Koyaushe ina girmama masarautarmu da Sarkin Musulmi musaman irin kokarin da yake yi na karade kasar nan don bukatar samar da zaman lafiya,” inji shi.
Wadanda suka halarci bikin sun hada da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Cif John Oyegun da Sakatarenta na kasa Mai Mala Buni da Gwamnonin jihohin Ribas da Osun da Kano da Kwara da Nasarawa da tsofaffin gwamnonin Zamfara da Nasarawa da Legas da Kwara Ahmad Yarima da Abdullahi Adamu da Bola Tinubu da Bukola Saraki da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Audu Obeh da Cif Bisi Akande da Kawu Baraje da sauransu.
Daga bangaren PDP akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da takwaransa na wakilai, sai dai wakili babu daga fadar Shugaban kasa.
Sauran wadanda aka nada a sarautun suna hada da Shugaban Majalisar Jihar Sakkwato Alhaji Lauwali Zayyana a matsayin Sarkin Gobir na Gwadabawa da Alhaji Aminu Abdullahi Iya, Iyan Sakkwato sai Alhaji Kabiru Tafida, Sarkin Fadar Sakkwato.