Jiga-jigan PDP 100 sun canza sheka zuwa APC a Jihar Edo
Wasu jiga jigan jam’iyyar PDP wadanda ake ji da su kimani mutum 100 suka canza sheka daga jam’iyyar PDP, inda suka koma jam’iyyar adawa ta APC a Jihar Edo cikin makon jiya. Kuma Gwamnan jihar Edo Comrade Adamu Aliyu Oshiomhole, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC ne suka hada hannu wajen karbar mutanen, wadannan mutane […]
Wasu jiga jigan jam’iyyar PDP wadanda ake ji da su kimani mutum 100 suka canza sheka daga jam’iyyar PDP, inda suka koma jam’iyyar adawa ta APC a Jihar Edo cikin makon jiya. Kuma Gwamnan jihar Edo Comrade Adamu Aliyu Oshiomhole, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC ne suka hada hannu wajen karbar mutanen, wadannan mutane wasu daga cikinsu sun fito ne daga yankin Oredo, wasu kuma daga karamar Hukumar Egor cikin jihar, da na wasu mazabu na Esant Eest da ogwa.
A jawabinsa wajen karbar mutanen, Gwamnan Jihar Edo, Comrade Adam Aliyu Oshiomhole ya ce, ‘ko wa ya kwana da sanin ce wa PDP wata jam’iyya ce, wadda ba za ta rabu da karairayin da take shirya wa mutane ba a duk lokaci, saboda haka ya kamata mu hada kai mu goyi bayan gaskiya, domin ci gabanmu da al’umma baki daya.
Gwamnan ya ce yau farin cikina shi ne, ganin mutane sun fara fahimta, tare da gane hanyar gaskiya, saboda haka babu batun karya ko wasu su yaudari jama’a a cikin harkar siyasa ko rayuwa, domin idan mutanen Najeriya sun waiwaya suka duba abin da ya wuce a baya za su ga cewa PDP ta zalunce su, tare da yi musu alkawuran karya ba kadan ba, a tsawon mulkin da ta yi wa al’ummar Najeriya rashin gaskiya, ta samu gindin zama da alkawurra da ba sa cikawa.
Yace jam’iyyar PDP ba za ta canza ba, domin lokaci ya kure musu, koda a ce suna son canzawa lamarin sai kara cakude musu, tunda da kansu sun san akwai bukatar canji. Saboda wannan ina matukar farin ciki da irin karbuwar da jam’iyyarmu ta APC take ci gaba da samu, musamman daga wadannan da suka fito daga Oredo da Egor, inda ya yaba musu da yi musu fatan su zama mambobi na kwarai a cikin jam’iyyar APC, domin ku bada labari ga wadanda ba sa nan. Kuma ku bai wa mara da kunya. Domin ada can baya kun sani a nan jihar ana fuskantar matsaloli, amma da muka zo sai Allah ya taimakemu muka canza kome, aka samu maslaha ta rayuwar al’ummar jihar baki daya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, jagoran ‘ya’yan jam’iyyar PDP din da suka canza shekar zuwa APC, Musta Festus Osaretin Obiawe, wanda yake daya daga cikin ‘yan majalisar jihar na yankin Oredo.
“Dalilin ficewar da muka yi daga PDP, shi ne, domin mun lura mun gane babu gaskiya ko adalci a cikin shirye-shiryenta gaba daya, ban da karairayi da yawan yaudarar jama’a, kawai shi ne ta sa agaba, don cimma manufofinta da burinta na cutar da al’ummar Najeriya. Wannan shi ne dalilinmu na canza sheka da muka yi zuwa APC,” inji shi’’.
Daga nan kuma sai Musta Obiawe ya gode wa Gwamna Oshiomhole da karbarsu da ya yi a cikin APC.
“Ina mai godiya ga Gwamana, saboda karbarmu da ya yi. Wannan ya tabbatar mana da cewa APC ba kamar irin PDP ba, wadda idan ba ka da wani babba da zai goya maka baya ba za a barka ka gudanar da komai ba a siyasar kasar nan ko da kana da kudi ballanta talaka, wanda ba su dauke shi a bakin komai ba.