Jigawa 2023: Wai mene ne zunubin Bahadeje ne?
Yankin ya ce tun 1999 bai taba yin Gwamnan Jihar ba.
A wannan mako wannan shafi yana dauke ne da rubutun da Alhaji Ahmed Ilallah Hadeja, imel: [email protected] ya aiko mana, yana korafi kan yadda aka ware yankinsa na Hadeja wajen fitar da ’yan takarar Gwamnan Jihar Jigawa tun dawowar mulkin farar hula sama da shekara 20 da suka gabata. Ga abin da yake cewa:
A yayin da aka soma kada gangar siyasa domin shiga kakar zaben shekara ta 2023, da alama a lisaffin siyasar bana ma a wajen nema wa Jigawa sabon ango, jagororin siyasar Jihar Jigawa ba sa kallon Jigawa-ta-Gabas, duk da kaifin sunan mutanen yankin wajen bayar da gudunmawa ga ci gaban jihar.
Hadeja, ko Masarautar Hadeja ita ce mazabar Sanatan Jigawa ta Arewa-maso-Gabas, mai kananan hukumomi takwas da suka hada da Auyo da Birniwa da Guri da Hadeja da Kafin Hausa da Kaugama da Kirikasamma da kuma Malam Madori.
A tarihin siyasar wannan lokacin tun daga kirikiro jihar kawo yau wannan yankin ne kadai bai taba jagorancin Jihar Jigawa da sunan Gwamna ba.
Hadeja ita cibiyar tattalin arzikin Jihar Jigawa, yankin ne da ke ba da sama da kashi 70 na arzikin da Jigawa ke samarwa a cikin gida, yankin Hadeja ne ya fi kowane yanki noma ridi da zobo (soborodo) a fadin Arewacin Najeriya. Yankin Hadeja ne ke kan gaba wajen noman shinkafa a Najeriya.
A takaice tattalin arzikin Jihar Jigawa wanda ya ta’allaka da noma, kusan akasarin noman ana yi ne a wannan yankin.
Kasuwar kifi da sauran naman-ruwa babu irin wannan kasuwar a fadin Arewa maso Yamma.
Amma har yau mutanen wannan yankin an ki aminta da su wajen ba da tasu gudunmawar a Jihar Jigawa. Abin tambaya shin mene ne zunubinsu? Fada da rashin cikawa, labarin fuska ya bambanta da na zuciya duk ba komai ba ne a halayen siyasar Najeriya.
A takaitaccen bincikena a kan mu’amalar Bahadeje da abokan zamansa musamman a cikin Jihar Jigawa, akasarin mutane sun nuna cewa Hadejawa mutane ne masu kawaici, kuma sukan hana nasu su ba wa bare, ba wai don ba sa son nasun ba, kawai don nuna kawaici.
Shin suna da kyama? Akasarin mutane sun nuna ba su da kyama, suna da son koya wa duk abokan aikinsu ko na kasa da su aiki da ilimin da suke da shi. Hakuri da iya mu’amala ya sa suke da alaka da dukkan manya a Jihar Jigawa da ma kasa baki daya.
Dukkan jagororin siyasar Jihar Jigawa a jiya da yau, suna tinkaho ne da mutanen wannan yankin wajen zame musu dakarai don cimma burinsu na siyasa, kuma sukan aminta da su har ma su zamanto masu fid-da-su kunya, a yayin da ake bukatar nagartattun mutane walau a tarayya koma a wajen tarayya.
To mene ne zunubinsu na kin amincewa da su wajen jagorar Jigawa don ba da tasu gudunmawar. A misali, Malam Sule Lamido a matsayinsa na babban jagoran PDP, a tsawon lokacin da PDP ta yi tana mulki tsakanin 1999 zuwa 2015, mutum bakwai da suka zamanto ministoci daga Jigawa biyar daga cikinsu duka sun fito ne daga yankin Hadeja.
A lokacin mulkin Malam Sule Lamido, ya yi alfahari da irin gudunmawar da mutannen yankin nan suka ba shi wajen samun nasara a mulkin da ya yi da ma ci gaban jam’iyyarsu ta PDP.
Amma ita Jama’iyyar PDP tun 1999 har zuwa 2019 ta juya wa wannan yankin baya wajen ba shi damar tsayar da dan takarar Gwamna a jam’iyyar.
Wannan mataki na PDP bisa jagorancin Sule Lamido ya ba wa kowa mamaki, kasancewar a yankin ne ya fi ko’ina magoya baya da ma dakaran siyasa da yake alfahari da su a ciki da wajen jihar waddanda har kawo yau suna tare da shi.
Har a wannan lokaci da aka soma kada gangar siyasar, alamu sun nuna cewa a wannan karon ma babu lissafin yankin Hadeja a takarar Gwamna a PDP. Tunda tuntuni har masu baki da kunu, kuma na kusa da shi Alhaji Sule Lamidon, sun yi azarbabi wajen bayyana wanda zai yi wa jam’iyyar takara a shekara mai zuwa.
An yi haka ne kuwa duk da cewa jam’iyyar ta PDP tana da fittatun mutane kuma kwararru ’yan siyasa da ya kamata su jira lokaci kafin yanke hukunci domin gudun abin da wannan riga-malam-masallaci ka iya jawowa.
Wannan na nuni da cewa har yanzu babu ma tunanin wannan yankin na Hadeja a gabansu. Shin ko mene ne zanubin wannan yankin da ake kokarin hana su takarar Gwamna har abada a wannan jam’iyya ta PDP?
Anya kuwa Jam’iyyar PDP tana lura da irin kaka-gidan da jam’iyya mai mulki take yi a wannan yanki na Hadeja kuwa? Me ya sa jagoran PDP a Jigawa ba ya tunanin cewa mutanen Hadeja za su iya fita daga lamarin jam’iyyar tunda sun ga shi ma ba ya lamarinsu a shekara 25 da Allah Ya ba shi damar fid-da- ’yan takarar jam’iyyar a Jigawa har sau bakwai?
Ko shi ma Mai girma Gwamna Mohammad Badaru Abubakar ya sake tabbatar da da kusancinsa, mu’amalarsa da kuma kawaicin mutanen wannan yankin da irin gudunmawar da suke ba shi da ma nuna masa kauna, a yayin da wata kungiya take martaba shi a garin Hadeja, wanda ya tabbatar da cewa babu wani Gwamnan da ya samu karbuwa a wajen mutanen Hadeja kamarsa.
Gwamna Badaru ya sake tabbatar da irin kishin kasa na al’ummar wannan yankin da kuma sadaukarwarsu, ya nuna cewa tunda yake a Gwamna babu wata kungiya daga wannan yankin da ta je masa don biyan bukatar mambobinta sai dai maganar a yi wa kasa da talakawa aiki, wanda wannan yunkuri ne na gyara kayanka, wannan ya taimaka masa wajen gina Jihar Jigawa.
To amma ita ma da alama kalangun da ake kadawa don taka rawa a Jam’iyyar APC, tana nuna alamun shirin kamar na jiya ne, hasashe na nunawa da kyar a ba wa mutanen wannan yankin damar taka tasu rawar, kuma hakan ba zai zo da mamaki ba ganin yadda yake neman nuna inda ya karkata.
To, koda su ma sauran al’umma Jigawa, wanda kowa ya aminta da cewa ana zaman lafiya da juna, kuma ci gaban jiharmu a yau ya fi jiya. Shin wane hange suke game da yadda wannan yankin na samun irin wannan matsayi marar dadi?
Shin bai zamanto abin tambaya cewa ba zahirin aminci da yarda da juna da zamantakewar ta gaskiya a tsakanin mutanen wannan jiha ba?
Ai idan ma wani laifi Kasar Hadeja ta yi wa sauran sassan Jihar Jigawa, to ya kamata a san cewa ba dukkan miliyoyin mutanen yankin ne suka aikata wannan laifi ba. Idan kuma wani hali ne na daban ake kallon mutanen yankin da shi, ya kamata a sani cewa babu yadda za a yi ka tara miliyoyin mutane kuma ka ce duk halayyarsu iri daya ce.
Tunda haka ne kuwa, to wane irin zunubi ne wannan yankin ya yi ta yadda sauran ’yan uwansa ba za su goya masa baya ba wajen ba da gudunmawarsa wajen gina wannan jiha? Ya kamata mai karatu ya tuna cewa mutanen wannan yanki ya goyi bayan mutanen Karamar Hukumar Birnin Kudu ta Kasar Dutse har sau uku sun zama gwamnoni (Ali Sa’ad sau daya, sai Sule Lamido sau biyu).
Yankin ya kara goyon bayan mutumin Kazaure har sau biyu ya yi Gwamna (Ibrahim Saminu Turaki).
A yanzu kuma sun goyi bayan mutumin Babura na Kasar Ringim har sau biyu shi ma ya zama Gwamna (Mohammed Badaru Abubakar). Jihar Jigawa mai al’umma iri daya, yare daya, addini daya kuma ’yan uwan juna, adalci shi ne kada a kafa ginshikin bambanci da wariya ga wani yankin don biyan bukatar wadansu mutane kalilan.
Allah Ya raya mana Jihar Jigawa abar alfaharinmu
Ahmed Ilallah Hadeja. [email protected]