Jigawa ce jiha ta biyu mafi nagartar mulki a Najeriya — Rahoto
Har ila yau, Jihar Jigawa ce ta zo ta biyu a ƙasar wajen gamsuwar al’umma da ayyukan gwamnati.
Jihar Jigawa ta zama ta biyu a faɗin Najeriya, kuma ta farko a jihohin shiyyar Arewa maso Yamma, a rahoton Phillips Consulting State Performance Index (pSPI) 2026 da ke auna nagartar mulki da ci gaban jihohi.
Bayanan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar a Dutse ranar Asabar.
Rahoton Philips Consulting (PCL) mai zaman kansa, ya nuna cewa Jigawa ta samu matsayi na biyu a Momentum Index, wanda ke tantance irin ci gaban da jihohi suka samu a binciken da ta gudanar, inda Jihar Enugu ce kaɗai ta fi ta matsayi.
An gudanar da binciken ne kan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja ta amfani da ma’aunai guda 37 da suka shafi nagartar mulki da kuma ci gaba.
Kashi 70 cikin 100 na binciken sun fito ne daga tantance bayanan kuɗaɗen gwamnati da sauran sahihan bayanai na hukumomi, yayin da kashi 30 cikin 100 suka fito daga ra’ayoyin al’umma.
A cewar rahoton, Jigawa ta samu maki +0.77 musamman a fagen inganta tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, ƙarancin bashi idan aka kwatanta da yawan jama’a, bunƙasar noma da kuma inganta ayyukan gwamnati.
Har ila yau, jihar ta zo ta biyu a ƙasar wajen gamsuwar al’umma da ayyukan gwamnati, inda ta samu maki 3.69 cikin 5, musamman a fannonin da suka haɗa da ingancin hanyoyi, tsaro da gaskiya da riƙon amana.
Rahoton ya kuma bayyana Jigawa a matsayin abin koyi wajen kyakkyawan mulki da tafiyar da kuɗaɗen gwamnati cikin hikima, yana mai nuni da cewa jihar na da mafi ƙarancin bashi idan aka kwatanta da yawan jama’arta.
Kazalika, rahoton na PCL ya nuna jihohin da suka fi samun ci gaba babu lallai su kasance a sahun gaba wajen samun kuɗaɗen shiga, sai dai waɗanda suka iya sarrafa albarkatun da suke da su yadda ya kamata ta hanyar nagartar mulki, gaskiya da riƙon amana da kuma aiwatar da kyawawan manufofi na ci gaba.