Jigawa ce kan gaba wajen inganta rayuwar talakawa – Osinbajo
Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Jihar Jigawa ita ce kan gaba a cikin jihohin kasar nan da ke koyi da tsarin tafiyar Gwamnatin Tarayya wajen inganta rayuwar talakawan Najeriya. Farfesa Osinbajo ya fadi haka ne a a ziyarar da ya kai jihar don sanya ido kan raba kayan tallafin aikin gona […]
Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Jihar Jigawa ita ce kan gaba a cikin jihohin kasar nan da ke koyi da tsarin tafiyar Gwamnatin Tarayya wajen inganta rayuwar talakawan Najeriya.
Farfesa Osinbajo ya fadi haka ne a a ziyarar da ya kai jihar don sanya ido kan raba kayan tallafin aikin gona ga manoma da kananan ’yan kasuwa da nufin tallafa wa marasa karfi a jihar a ranar Talatar da ta gabata.
Mataimakin Shugaban Kasar ya kara da cewa abin da ya gani da idonsa a Jigawa wani lamari ne da yake cike da sako da zai isar wa Fadar Shugaban Kasa. Ya ce Jihar Jigawa ta ciri tuta wajen aiwatar da shirin tallafa wa mata da yara da matasa da marasa karfi wajen ba da tallafin Npower da bunkasa aikin noma.
Farfesa Osinbajo ya ci gaba da cewa tsarin Gwamnatin Jigawa yana tafiya kafada-da-kafada da tsarin Gwamnatin Tarayya na inganta rayuwar talakawa.
“Gwamnatin Tarayya tana bai wa mutun dubu 37 tallafin Naira dubu biyar-biyar duk wata, kuma sama da mata dubu 37 suka samu aikin yi da suka hada da dafa wa yara ’yan makarantar firamare abinci a makarantun da ke fadin kasar nan. Kuma ya kamata gwamnonin Najeriya su yi koyi da Gwamnatin Jihar Jigawa wajen tallafa wa talakawa a yankunansu,” inji shi.
Gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Badaru, ya shirya bai wa zawarawa da matan da mazansu suka rasu su 2,850 rancen awakin kiwo uku-uku a matsayin jari don tallafa wa matan da nufin dogara da kansu.
Gwamna Badaru ya kara da cewa matasa kimanin dubu 34 da 635 maza da mata suka amfana daga tallafin gwamnatin jihar na inganta rayuwar matasan jihar.