Jigawa Golden Stars ta kori kocinta

Kungiyar Kwallon Kafa ta Jigawa Golgen Stars ta kori mai horar da ’yan wasanta Malam Rabiu Tata, tare da maye gurbinsa da Gilbert Opana. Kungiyar ta yanke wannan hukunci ne bayan da ta samu  koma-baya a gasar Firimiya ta kasa ta bana da take fafatawa. A ranar Litinin Jigawa ta buga 1-1 da Ribers United […]

Jigawa Golden Stars ta kori kocinta

Kungiyar Kwallon Kafa ta Jigawa Golgen Stars ta kori mai horar da ’yan wasanta Malam Rabiu Tata, tare da maye gurbinsa da Gilbert Opana. Kungiyar ta yanke wannan hukunci ne bayan da ta samu  koma-baya a gasar Firimiya ta kasa ta bana da take fafatawa.

A ranar Litinin Jigawa ta buga 1-1 da Ribers United a wasan mako na 16, inda hakan ya sa ta koma ta 18 cikin a teburi da maki 14.

Mannir Adamu Kazaure shi ne Sakataren Kungiyar ya shaida wa BBC cewar Rabi’u Tata karamin koci ne ba zai iya kai Jigawa matakin da suke fata ba.

Ya ce tun baya sun yi hakuri su ga iya gudun ruwansa, amma sun lura cewa matakin Firimiya ya fi karfinsa.

Jigawa wadda ta buga wasa 15 a kakar bana ta ci wasa hudu da canjaras biyu aka doke ta a fafatawa tara, inda ta ci kwallo 15 aka zura mata 23 a raga.

Gilgert Opana wanda ya maye gurbin Rabiu Tata, tsohon dan wasan Jigawa ne ya kuma horar da ita a baya. Rabi’u Tata shi ne ya hawo da Jigawa zuwa gasar Firimiya ta Najeriya ta bana.