Jigawa: Gwamnati ta kashe N7bn don tallafa wa ma’aikata su yi noma

Gwamnatin ta ce ta samar da shirin ne da nufin samar da wadataccen abinci a jihar.

Jigawa: Gwamnati ta kashe N7bn don tallafa wa ma’aikata su yi noma

Gwamnatin Jihar Jigawa, ta ce ta kashe kusan Naira biliyan bakwai wajen aiwatar da Shirin Tallafa wa Ma’aikatan Gwamnati ta Fuskar Noma (JSWAP), inda sama da ma’aikata 17,000 suka amfana da shirin tun daga matakin farko zuwa na uku.

An bayyana hakan ne a lokacin da aka fara rabon kayan aikin noma na mataki na huɗu na daminar 2026.

An gudanar da taron ne a harabar Kamfanin JASCO da ke Dutse.

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda Mataimakinsa, Injiniya Aminu Usman, ya wakilta, ya ce shirin na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatinsa na inganta rayuwar ma’aikata da kuma bunƙasa noma domin samar da isasshen abinci a jihar.

Ya ce shirin yana bai wa ma’aikatan gwamnati damar samun rance don yin noma da kayan aikin gona, domin su ƙara samun kuɗin shiga tare da taimakawa wajen samar da abinci.

Shugaban Majalisar Tattaunawar Ma’aikatan Gwamnati (JPSNC), Kwamared Yusha’u Abubakar, ya ce gwamnatin jihar ta zuba kusan Naira biliyan bakwai a cikin shirin tun daga matakin farko zuwa na uku.

Ya ce sama da ma’aikata 17,000 sun ci gajiyar shirin, tare da yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa yadda yake ba da muhimmanci ga walwalar ma’aikata da ci gaban harkar noma.

A cewarsa, yadda ma’aikata ke mayar da rancen da suka karɓa ya sa shirin ke ci gaba da taimaka wa sababbin masu amfana a kowace damina.

“Muna alfahari da cewa wannan shi ne shirin rancen noma mafi nasara da aka taɓa gudanarwa a tarihin Jihar Jigawa,” in ji Yusha’u.

Ya kuma yaba wa Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke kula da shirin, bisa yadda yake jagorantar shirin bisa gaskiya da riƙon amana.

Shi ma Dagaceri ya ce nasarar shirin ta samo asali ne daga kyakkyawan shugabanci da hangen nesan gwamnan jihar.

Ya bayyana cewa dawo da kuɗaɗen rancen da aka bayar a baya ya sa aka ci gaba da gudanar da shirin ba tare da matsala ba, tare da bai wa ƙarin ma’aikata damar amfana.

Ya ƙara da cewa fara mataki na huɗu na shirin daminar 2026 wata alama ce ta ci gaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen inganta rayuwar ma’aikata, bunƙasa noma da tabbatar da wadatar abinci.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan majalisar dokoki, shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago, sakatarori, shugabannin hukumomi da ma’aikatan gwamnati daga sassa daban-daban na jihar.

An kammala taron da fara rabon kayan aikin noma ga ma’aikatan gwamnati da suka ci gajiyar shirin daminar 2026.