…Jigawa kuma mutum 2,369 za su sauke farali bana
Daraktan Shirye-Shirye na Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa Dokta Umar Labbo ya ce kimanin maniyyata 2, 369 ne ake sa ran za su halarci aikin Hajjin bana daga jihar.Dokta Umar Labbo ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke harabar hukumar, inda ya ce Hukumar Hajji ta kasa […]
Daraktan Shirye-Shirye na Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa Dokta Umar Labbo ya ce kimanin maniyyata 2, 369 ne ake sa ran za su halarci aikin Hajjin bana daga jihar.
Dokta Umar Labbo ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke harabar hukumar, inda ya ce Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta bai wa jihar kujera 2,369 domin sauke farali a bana.
Ya ce tuni suka kammala tantance maniyyatan jihar da suka biya kudinsu domin yin aikin Hajjin bana “Tuni Hukumar Alhazan ta tanadi masaukin alhaza a kasa Mai tsarki a kusa da Harami,” inji Daraktan.