Jigawa na samar da kashi 40 na alkamar da ake nomawa a Najeriya – Shettima

Shettima ya ce kowace jiha tana da rawar da za ta taka wajen bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.

Jigawa na samar da kashi 40 na alkamar da ake nomawa a Najeriya – Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Jihar Jigawa na samar da kusan kashi 40 cikin 100 na alkamar da ake nomawa a Najeriya.

Ya kuma bayyana jihar a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da ke da damar jawo masu zuba jari a fanni noma, makamashi da masana’antu.

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin buɗe taron Jigawa State Economic and Investment Summit (J-INVEST 2026) da aka gudanar a Dutse.

Ya ce bunƙasar tattalin arziƙin Najeriya ba aikin Gwamnatin Tarayya kaɗai ba ne, kowace jiha na da rawar da za ta taka ta hanyar amfani da albarkatun da take da su.

Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnati ta yi sun fara ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa.

Ya bayyana cewa sauye-sauyen da aka yi a tsarin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje, Dokar Sauƙaƙa Harkokin Kasuwanci da sauran gyare-gyare sun taimaka wajen sauƙaƙa fara kasuwanci da inganta yanayin zuba jari a ƙasar.

Shettima, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, saboda ƙoƙarinsa na bunƙasa noma da jawo masu zuba jari.

Ya ce baya ga alkama, Jigawa na daga cikin manyan jihohin da ke samar da sesame da ake fitarwa zuwa ƙasashen waje, inda sama da manoma 4,000 ke cin gajiyar shirin out-growers.

Sai dai ya buƙaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su ƙara zuba jari a injinan noma, ingantattun iri, ban ruwa, taki, horas da manoma da kuma amfani da fasahohin zamani.

Ya kuma ce Dokar Wutar Lantarki ta 2023 ta bai wa jihohi damar samarwa da rarraba wutar lantarki, wanda zai taimaka wajen bunƙasa masana’antu.

A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi, ya ce an shirya taron ne domin jawo sabbin masu zuba jari da samar da ayyukan yi a jihar.

Ya ce kasafin kuɗin Jigawa na 2026 ya kai kusan Naira biliyan 902, kuma an ware sama da kashi 76 cikin 100 na kuɗin domin ayyukan raya ƙasa.

Namadi, ya ce tun daga shekarar 2024, jihar ta samu nasarar jawo sabbin masu zuba jari 64 a fannoni daban-daban, ciki har da noma, makamashi da masana’antu.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da filaye sama da hekta 13,000 ga masu zuba jari, tare da bayar da kwangilar gina hanyoyi sama da kilomita 1,300 domin inganta kasuwanci da sufuri.

Gwamnan, ya yi kira ga masu zuba jari da cibiyoyin kuɗi su yi amfani da damammakin da Jigawa ke da su, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ba su cikakken goyon baya.

Taron J-INVEST 2026 ya samu halartar ministoci, gwamnoni, ’yan majalisu, jakadun ƙasashe, shugabannin masana’antu, cibiyoyin kuɗi da masu zuba jari daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje.