Jigawa ta biya diyyar Naira miliyan 442 ga madwabtan Jami’ar Tarayya
Gwamnatin Jihar Jigawa ta biya diyyar Naira miliyan 442 da dubu 531 da 49 kan gonaki da gidajen da suka fada cikin taswirar mazaunin dindindin na Jami’ar Tarayya da ke dauyen Magorawa a kusa da Dutse fadar jihar.Babban Sakatare a Ma’aikatar dasa da Safiyo ta Jihar Alhaji Nasiru Muhammed ne ya shaida wa manema labarai […]
Gwamnatin Jihar Jigawa ta biya diyyar Naira miliyan 442 da dubu 531 da 49 kan gonaki da gidajen da suka fada cikin taswirar mazaunin dindindin na Jami’ar Tarayya da ke dauyen Magorawa a kusa da Dutse fadar jihar.
Babban Sakatare a Ma’aikatar dasa da Safiyo ta Jihar Alhaji Nasiru Muhammed ne ya shaida wa manema labarai haka lokacin da yake mida cakin kudin a fadar Hakimin garin Dutse Alhaji Jamilu Muhammed Basiru Sunusi.
Ya shawarci wadanda suka amshi kudaden su yi amfani da su wajen inganta rayuwarsu maimakon facaka da su. Kuma ya gode musu saboda hadin kan da suka ba su yayin amsar diyyar tun daga lokacin da gwamnatin jihar ta amshi gidajensu da gonakin ta mida wa jami’ar a matsayin matsuguninta na dindindin domin tabbatar da harkokin karatu a jami’ar.
Da yake nasa jawabin Turakin Dutse Kuma Hakimin garin Dutse Alhaji Jamilu Muhammed Sunusi ya gode wa mutanen yankin da suka amshi diyyar tare da yaba wa gwamnatin jihar saboda dodarinta na cika aldawarin da ta dauka wajen biyan diyyar.
Shugaban Jami’ar Farfesa Jibiril dahiru Aminu ya yaba wa al’ummar yankin na Magorawa da sauran wadanda abin ya shafa.