Jigawa ta dukufa wajen inganta karatun nakasassu
Gwamnatin Jahar Jigawa ta bude cibiyoyin ci gaba da karatu ga daliban da suka sami wata matsala ba su kammala karatun sakandare ba guda tara a daukacin mazabun sanata guda uku, yayin da aka bude cibiyoyi uku a kowace mazaba ta sanata dake jahar. Jawabin hakan ya fito ne daga bakin babban sakataren hukumar ilimin […]

Gwamnatin Jahar Jigawa ta bude cibiyoyin ci gaba da karatu ga daliban da suka sami wata matsala ba su kammala karatun sakandare ba guda tara a daukacin mazabun sanata guda uku, yayin da aka bude cibiyoyi uku a kowace mazaba ta sanata dake jahar. Jawabin hakan ya fito ne daga bakin babban sakataren hukumar ilimin manya na jahar Jigawa, Malam Abbas A Abbas.
Abbas ya ce sun baiwa daliban da suka kammala karatun sakandare 6,800 akan fannoni daban-daban domin su sami damar dogaro da kansu tare da sanin dabarun zana jarabawa, yayin da aka baiwa ma’aikatan hukumar horo na musamman domin sanin makamar aiki akan fannoni daban-daban.
Ya ce sama da mutun 160 ne suka sami cin gajiyar al’amarin kuma hukumar ta kashe sama da naira dubu 927 wajen sayen kayan aiki da suka hada da kwamfutoci da injinan majigi da na yin kwafi takardu da na’urar daukar hoto da kwamfuta ta hannu.
Ta baiwa makafi rakoda 700 tare da littatafan rubutu guda 2,000 ga guragu su kuma zabiya aka ba su litatafai 1,000.
Haka zalika hukumar ta baiwa wadanda suke tsare a gidan yari kayan karatu da suka hada da allunan koyan karatu 20, katan na alli 10, littatafan koyan rubutu 5,000 da kuma gudumawar fansira 2,000 yayin da su ma makarantun yaki da jahilci dake cikin al’umma wadanda ba na gwamnati ba, an ba su kayan koyarwa da nufin inganta harkokin karatun a daukacin makarantun.