Jigawa ta gano malaman bogi 1,700

Hukumar Ilimi Bai-daya (SUBEB) ta Jihar Jigawa ta ce ta gano malaman bogi 1,700 da suke aiki da jabun takardun koyarwa a jihar.Shugaban hukumar ta SUBEB Alhaji Salisu Zakar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da hukumar ta kira a makon jiya inda ya ce tuni gwamnatin jihar ta kafa wani kwamati […]

Jigawa ta gano malaman bogi 1,700
Jigawa ta gano malaman bogi 1,700

Hukumar Ilimi Bai-daya (SUBEB) ta Jihar Jigawa ta ce ta gano malaman bogi 1,700 da suke aiki da jabun takardun koyarwa a jihar.
Shugaban hukumar ta SUBEB Alhaji Salisu Zakar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da hukumar ta kira a makon jiya inda ya ce tuni gwamnatin jihar ta kafa wani kwamati mai karfi da zai tantance sahihancin takardun malaman da ake zargi da jabun takardun tare da daukar mataki a kan duk malamamin da aka samu da laifin aron takardun wani ko takardun jabu.
Alhaji Zakar ya kara da cewa daga yanzu duk malamin makarantar da gwamnatin jihar ta tura karatu ya zama dole a wajensa a duk hutun shekara ya rika gabatar da takardar shaidar jarrabawarsa ta karshen zangon karatu ga Hukumar SUBEB domin sanin halin da yake ciki a makarantar.
Ya kara da cewa daga shigarsu gwamnati an kara wa malamai 1,662 girma, yayin da aka bai wa malamai sama da 3,000 horo a bangarori daban-daban.
Shugaban ya ce a bana hukumar za ta dauki malaman makaranta 4,500, bayan an gama tantance malaman da ake zargi da aron takardun koyarwa da masu na bogi, sai daia ya gargadi jama’a su guji masu cutar jama’a da suke amfani da wannan dama wajen yi musu damfara.
Ya ce gwamnatin jihar za ta kashe Naira biliyan daya da miliyan 200 wajen gyare-gyaren makarantu da
sayen kayan karatu a bana.