Jigawa ta horar da Malaman Gona da Gandun Daji

Kimanin Malaman Gona da Ma’aikatan Gandun Daji 81 aka shiryawa bitar sanin makamar aiki dake karkashin kulawar kananan hukumomi a Jahar Jigawa. Bitar wadda kamfanin Continuen Professional Debelopment na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano tare da hadin gwiwar ma’aikatar kananan hukumomin jahar ta shirya a dakin taro na cibiyar horar da ma’aikata ta jiha […]

Jigawa ta horar da Malaman Gona da Gandun Daji

Kimanin Malaman Gona da Ma’aikatan Gandun Daji 81 aka shiryawa bitar sanin makamar aiki dake karkashin kulawar kananan hukumomi a Jahar Jigawa. Bitar wadda kamfanin Continuen Professional Debelopment na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano tare da hadin gwiwar ma’aikatar kananan hukumomin jahar ta shirya a dakin taro na cibiyar horar da ma’aikata ta jiha a ranar Larabar da ta gabata.

Alhaji Kabiru Sugungun shi ne Babban Sakatare a Hukumar Lura da Walwalan Ma’aikatan kananan Hukumomin Jahar ta Jigawa wato Local Gobernment Serbice Commission ya ce gwamnatin jahar ta kashewa naira miliyan hudu da dubu hamsin wajen baiwa ma’aikatan 81 horo da aka zabo su daga kananan hukumomin jahar 27.

Ya ce an dauko mutun uku daga kowacce karamar hukuma a jahar ta Jigawa wadanda suka hada da malaman gandun daji da malaman gona da kuma shugabannin bangarorin aikin gona wato HODs wadanda yawansu ya kai adadin mutun 81.

Sugungun ya ce kowanne mutun daya an kashe masa naira dubu 50 wajen ba shi horon da ake bukata. Da yake bude bitar, ya hori daukacin mahalarta bitar da su yi amfani da abinda suka koya a zamanin bitar. Ya kuma kara da cewar yana da tabbacin cewar wadanda aka zabo din domin ba su horon, zasu baiwa mara-da kunya akan al’amarin wajen yin aiki da abinda suka koya a aikace, ya kuma shawarce su da su tattauna sosai akan abinda aka gwada masu duk inda ba su gane ba, su tambaya ayi masu karin haske. Ya kuma hore su da su yi amfani da dabarun da suka koya wajen tattara bayanan da za su baiwa manoma, kasancewar yanzu lokaci ne na noma domin bawa manoma shawarwarin da za su amfane su. 

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu