Jigawa ta kasafta kashe Naira Biliyan 134 a bana

Gwamnatin Jigawa za ta kashe Naira biliyan 134.17 a kasafin kudin da ta ware na shekarar 2018.   Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar a lokacin da yake karanta jawabin kasafin kudin na bana a majalissar dokokin jahar ta a ranar Talatar da ta gabata. Kamar yadda gwamnan ya […]

Jigawa ta kasafta kashe Naira Biliyan 134 a bana

Gwamnatin Jigawa za ta kashe Naira biliyan 134.17 a kasafin kudin da ta ware na shekarar 2018.   Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar a lokacin da yake karanta jawabin kasafin kudin na bana a majalissar dokokin jahar ta a ranar Talatar da ta gabata.

Kamar yadda gwamnan ya fada, kashe mafi tsoka na kasafin kudin wannan shekarar zai tafi ne a wajen aikin gona sai harkar ilimi da lafiya suka marawa aikin gona baya yayin da sauran kaso na kudin zai tafi wajan aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa a fadin jahar ta Jigawa.

Da ya juya wajen kudaden shiga kuwa, cewa ya yi a na sa ran jahar za ta sami kimanin naira biliyan 10 da miliyan 500. Haraji kuma ana sa ran zai ja naira biliyan 51.63, yayin da wasu ayyuka na musamman zasu ja naira biliyan 4.4. Yayin da basussuka zasu ja kimanin naira 6.23 sauran alawus-alawus na ma’aikatan gwamnatin jahar zasu cinye naira biliyan daya da miliyan 600, duka duka daga cikin kudaden da gwamnatin jahar ta ware a bana.

Haka kuma gwamnatin jahar ta ware naira biliyan 65.6 domin biyan kudaden ayyukan lura da ofisoshi ko tafiyar da ayyukan ofisoshin gwamnati, yayin da aka ware naira biliyan 67.035 domin aiwatar da manyan aiyuka. Yayin da gwamnatin jahar ta ware sama da naira biliyan biyu domin inganta harkar noma don riba, a wani shiri na Closter Farming, wanda gwamnatin tarayya ta bullo da shi da nufin taimakawa rayuwar matasa a fadin kasar.

Gwamna Badaru ya kara da cewar ragowar kudaden da suka rage gwamnati za ta kashe su ne wajen karasa ayyukan baya da suka fara ba su kammala ba. Ya ce kashi 10 na kudin da lafiya za ta lashe zai tafi ne wajan gyaran asibitocin jahar manya da kanana tare da inganta mahallin malaman asibitocin jahar da kuma samar da abinci mai gina jiki, domin amfanin yara kanana da kuma samar da wuta a daukacin asibitocin jahar kuma za a samar da karin sabbin asibitoci a fadin jahar a kokarin gwamnatin jahar na bunkasa harkokin kiwon lafiya.

Haka kuma gwamnatin tasa ta ware wa yankunan karkara naira biliyan 2.6biliyan yayin da manyan garuruwa aka ware masu naira biliyan 1.5 yayin da su kuma kananan hukumomi aka ware masu naira biliyan 56.49, domin gudanar da dukkanin ayyukan da suka shafi kananan hukumomin jahar kai tsaye.

Da yake amsar kasafin kudin na bana, Shugaban Majalissar dokokin jahar ta Jigawa, Hon. Idris Isah Gwaram ya ce majalissar dokokin jahar ta amshi kasafin kudin na bana da hannu biyu kuma za ta yi nazarinsa ba tare da bata lokaci ba, kuma za su sanya kasafin kudin na bana hannu domin a sami damar yi wa talakawa aikin da ya dace.

Ya kara da cewar majalissar za ta yi wa kundin kasafin kudin na bana karatu cikin hanzari, domin ita ma gwamnatin jahar ta sami damar yi wa jama’ar jahar ayyukan da ta sa a gabanta.