Jigawa ta kashe Naira biliyan biyu kan gina gidan rediyo da talabijin

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bude gidan rediyo da talabijin mallakar jihar da aka kashe sama da Naira biliyan biyu wajen gina shi da sanya masa kayan aiki na zamani. Kwamashinan Watsa Labarai na Jihar Alhaji Babandi Ibrahim Gumel ne ya sanar da manema labarai a wajen kaddamar da gidan rediyo da talabijin […]

Jigawa ta kashe Naira biliyan biyu kan gina gidan rediyo da talabijin
Jigawa ta kashe Naira biliyan biyu kan gina gidan rediyo da talabijin

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bude gidan rediyo da talabijin mallakar jihar da aka kashe sama da Naira biliyan biyu wajen gina shi da sanya masa kayan aiki na zamani.

Kwamashinan Watsa Labarai na Jihar Alhaji Babandi Ibrahim Gumel ne ya sanar da manema labarai a wajen kaddamar da gidan rediyo da talabijin din a ranar Larabar makon jiya, inda ya ce gidan talabijin din za a rika kama shi a daukacin jihar domin an kafa karin tashoshi masu cin nisan zango a Kazaure da Hadeja domin jama’ar jihar su samu damar kama tashar kamar yadda suke sauraran rediyon Jigawa a sassan jihar
Kwamishinan ya ce ba ma Jihar Jigawa ba makwabtan jihar da dama za su rika kama tashar talabijin din don kallo da sauraren yadda al’amuran suke gudana a duniya.
Ya ce jama’ar Jihar Jigawa za su jima ba su manta da Gwamna Lamido ba, saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen habaka jihar.
Kwamishina Babandi ya ce gwamnatin ta kashe kimanin Naira biliyan biyu da miliyan 124 wajen gina gidan rediyo da talabijin din tare da sanya masa kayan aiki na zamani da kuma gyare-gyaren da aka yi wa sauran tashoshin watsa labarai da ke Kazaure da Hadeja.