Jigawa za ta ba zawarawa 8,600 bashin awaki

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ce zai taimaka wa zawara dubu takwas da 610 da bashin awaki domin su yi kiwo. Gwaman Muhammad Badaru ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati inda ya ce za a zabo zawarawan ne daga cikin mazabu 287 da ke […]

Jigawa za ta ba zawarawa 8,600 bashin awaki
Jigawa za ta ba zawarawa 8,600 bashin awaki

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ce zai taimaka wa zawara dubu takwas da 610 da bashin awaki domin su yi kiwo. Gwaman Muhammad Badaru ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati inda ya ce za a zabo zawarawan ne daga cikin mazabu 287 da ke jihar inda za a zabi zawarawa 25 zuwa 30 daga kowace mazaba. Gwamna Badaru ya ce kowace bazawara za a ba ta akwaki biyu wadanda za ta kiwata kuma gwamnatin za ta ci gaba da taimaka wa zawarawan har tsawon shekara biyu masu zuwa. Ya ce an fito da tsarin tallafa wa zawarawan ne da nufin taimaka wa matan da suka rasa mazajensu alhali an bar su da kananan yara a kokarin gwamnatin na tallafa wa mata da marayun don su samu ikon dogaro da kansu ta yadda yaran za su samu damar yin karatu da ciyar da kansu. Ya ce za su taimaka wa matan da kiwon awakin ne saboda kiwon awakin ya fi sauki da kawo riba cikin kankanen lokaci. “Mun dauki aniyar bai wa mata tallafin awakin ne domin su dogara da kansu saboda mafiya yawan jama’ar da za su amfana da kiwon jama’ar karkara ne kuma yana da riba mai yawa,” inji Gwamnan.