Jigawa za ta dasa itatuwan dalbejiya miliyan biyu a iyakarta da Nijar

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya kaddamar da shirin dashen itatuwa na bana inda ya ce jihar za ta dasa itatuwa miliyan biyu a kan iyakarta da Jamhuriyar Nijar.Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abdulkadir Fanani ya wakilta ya bayyana haka ne lokacin kaddamar da shirin a karamar Hukumar Kiyawa, inda ya gargadi […]

Jigawa za ta dasa itatuwan dalbejiya miliyan biyu a iyakarta da Nijar
Jigawa za ta dasa itatuwan dalbejiya miliyan biyu a iyakarta da Nijar

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya kaddamar da shirin dashen itatuwa na bana inda ya ce jihar za ta dasa itatuwa miliyan biyu a kan iyakarta da Jamhuriyar Nijar.
Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abdulkadir Fanani ya wakilta ya bayyana haka ne lokacin kaddamar da shirin a karamar Hukumar Kiyawa, inda ya gargadi al’ummar jihar su guji sare itatuwa da kone daji ba bisa ka’ida ba.
Gwamnan ya ce gwamnati ba za ta sanya ido wasu mutane su rika sare itatuwa suna bai wa hamada damar kwararowa ba, inda ya ce gwamnatin za ta sanya kafar wando daya da duk wanda aka kama yana sare itatuwa ba bisa ka’ida a jihar.
Ya ce gwamnatin jihar za ta farfado da gandun daji a daukacin kananan hukumomin jihar a kokarinta na kare barazanar kwararowar hamada a karkashin wani shiri da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi da ake yi wa take koriyar Katanga (GGW).
Ya ce Jihar Jigawa tana cikin jihohi 11 da aka ware a Arewa da suke fuskantar kwararowar hamada da hakan ke yi wa harkar noma barazana kuma na taimaka wa wajen lalata muhalli tare da sanya jama’a yin kaura zuwa wasu sassan kasar nan masu dausayi.
Gwamna Badaru ya ce “Gwamnatin Jigawa ta ware kilomita 250 da za ta dasa itatuwan dalbejiya da sauran itatuwa a kan iyakar kasar nan kuma za a dasa itatuwa miliyan biyu a daukacin kananan hukumomin jihar musamman wadanda suke makwabtaka da kasar Nijar.”
Ya ce dashen gandun dajin na Koriyar Katanga da jihar ta za ta yi mai tsawon kilomita 250 zai fara ne daga kauyen Tukwikwi a yankin Masarautar Hadeja da ke gabashin jihar ya kare a kauyen Rorau a karamar Hukumar Roni da ke yammacin jihar.
Gwamna Badaru ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa Ma’aikatar Kula da
Muhalli ta Jihar tallafi a kan shirin yaki da hamada don ganin shirin ya kai ga nasara tare da hadin gwiwar kananan hukumomin jihar 27.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Alhaji Sabo Wada Ringim ya ce gwamnatin jihar ta bullo da shirin ne da nufin cusa wa jama’a da’a a cikin zukata da kuma kishin raya muhalli tare da koya musu yadda za su yaki da kwararowar hamada a yankunansu.