Jigawa za ta kashe Naira biliyan 14 kan gyaran hanyoyi

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba da kwangilar aikin hanyoyin cikin gari a wasu manyan garuruwa 10 da ke jihar a kokarinta na inganta rayuwa mazauna manyan garuruwa tarew da matso dagwamnati kusa da jama’a.Kwamashinan Watsa Labarai na Jihar Jigawa Alhaji Babandi Ibrahim Gumel ne ya sanar da manema labarai haka bayan kammala zaman Mjalisar Zartarwar […]

Jigawa za ta kashe Naira biliyan 14 kan gyaran hanyoyi
Jigawa za ta kashe Naira biliyan 14 kan gyaran hanyoyi

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba da kwangilar aikin hanyoyin cikin gari a wasu manyan garuruwa 10 da ke jihar a kokarinta na inganta rayuwa mazauna manyan garuruwa tarew da matso da
gwamnati kusa da jama’a.
Kwamashinan Watsa Labarai na Jihar Jigawa Alhaji Babandi Ibrahim Gumel ne ya sanar da manema labarai haka bayan kammala zaman Mjalisar Zartarwar Jihar a shekaranjiya Laraba.
Ya ce za a gina hanya mai tsawon kilomita 12 da digo 4 kan Naira biliyan biyu da miliyan 300, sai hanyar cikin garin Kazaure mai tsawon kilomita 12 da digo 6 da za a yi ta a kan Naira biliyan
biyu da miliyan 900, yayin da za a kashe Naira biliyan daya da miliyan 900 don gina hanyoyi masu tsawon kilomita 10 a garin Gumel.
Sauran sun hada da gina hanyoyin cikin gari a garin Malam Madori da Kafin Hausa da Maigatari da Guri da Sule Tankarkar da sauransu.
Kamfanoni goma ne gwamnatin jihar ta amince su gudanar da aikin gwangilar hanyoyin a garuruwa goma ciki har da Hadejia Consultant Engenearing Company da
Kamfanin Chaina na CGC da wani sabon kamfani mai suna Kaf Enginearing Company.
Kwamshina Babandi ya kara da cewa gwamnatin jihar ta amince da gina hanyar Tasheguwa zuwa Guri a kan Naira miliyan 431 da kuma gyara hanyar Kazaure zuwa Roni da ta Bamaina zuwa Nasaru da ke cikin Jihar Bauchi.