Jigawa za ta kashe Naira biliyan uku don inganta karkara
Gwamnatin Jihar Jigawa da hadin kungiyar kungiyyoyin NAIF da DFID da kuma Gwamnatin Tarayya sun dukufa wajen inganta rayuwar mutanen karkarar jiharta mayar da hankali wajen samar da hanyoyin mota da sauransu.Kwamashinan Raya Karkara da Birane, Alhaji Muhammed Sunusi Gako ne ya fada wa manema labarai haka a lokacin da ya kira taron manema labarai […]
Gwamnatin Jihar Jigawa da hadin kungiyar kungiyyoyin NAIF da DFID da kuma Gwamnatin Tarayya sun dukufa wajen inganta rayuwar mutanen karkarar jihar
ta mayar da hankali wajen samar da hanyoyin mota da sauransu.
Kwamashinan Raya Karkara da Birane, Alhaji Muhammed Sunusi Gako ne ya fada wa manema labarai haka a lokacin da ya kira taron manema labarai a Dutse, inda ya ce
da zarar an kammala aikin hanyoyin mota a yankunan karkara za a mika hanyoyin ga jama’a da hanyoyin ke yankunansu don kula da su, inda za su rika amfani da kungiyoyin aikin gayya suna gyara hanyoyin idan bukata ta taso.
Alhaji Sunusi ya ce gwamnatin jihar tana yin hanyoyin mota a yankunan karkara da suka yi daidai da zamani koda za a bukaci kara fadinsu a nan gaba. Ya ce kofarsa a bude take wajen taimaka wa kungiyoyin aikin gayya da ke jihar musamman na yankunan karkara don samar da makarantun Islamiyya da gyaran masallatai da gina magudanun ruwa da kwalbati a yankunan karkara da manyan biranen jihar.
Ya ce gwamnatin jihar tana nan tana shirin hada kauyuka zuwa matakin birane a kokarin hukumar na samar da manyan garuruwa a jihar wanda hakan zai taimaka wajen kusantar da gwamnati cikin sauki ga jama’a kuma hakan zai taimaka talakawa su samu ikon cin moriyar siyasa da ayyukan gwamnati cikin sauki.
Alhaji Gako ya ce za a fara samar da samfurin garuruwa a yankunan masarautun jihar biyar a matsayin garuruwan misali tuni gwamnatin jihar ta ware Naira miliyan 1,700 wajen samar da ruwan sha a yankunan karkara kuma hukumar za ta kashe Naira miliyan 700 wajen samar da wutar lantarki.