Jigawa za ta kashe Naira miliyan tara a gasar karatun Alkur’ani na bana

Gwamnatin Jhar Jigawa za ta kashe Naira miliyan tara (N9m) wajen daukar nauyin gasar masabakar karatun Alkur’ani na bana karo na 30 da yake gudana a garin Dutse da nufin tallafa wa daliban da kuma hukumar gudanarwar shirya gasar&nbsp na bana.Kwamishiniyar ilimi ta Jihar Jigawa Hajiya Rabi Ishak ce ta fadi haka a wajen bikin […]

Jigawa za ta kashe Naira miliyan tara a gasar karatun Alkur’ani na bana
Jigawa za ta kashe Naira miliyan tara a gasar karatun Alkur’ani na bana

Gwamnatin Jhar Jigawa za ta kashe Naira miliyan tara (N9m) wajen daukar nauyin gasar masabakar karatun Alkur’ani na bana karo na 30 da yake gudana a garin Dutse da nufin tallafa wa daliban da kuma hukumar gudanarwar shirya gasar&nbsp na bana.
Kwamishiniyar ilimi ta Jihar Jigawa Hajiya Rabi Ishak ce ta fadi haka a wajen bikin bude gasar karatun masabakar ta bana da ke gudana a Kwalejin Kimiyya da Fusaha na Jihar a ranar Talatar da ta gabata.
Hajiya Ishak ta kara da cewa gwamnatin jihar za ta kashe Naira miliyan hamsin da tara&nbsp (N59m) wajen daukar nauyin daliban da suka zama zakara a fagen gasar ta bana wanda za a tura su don yin karatun digiri a jami’o’in kasashen waje domin samar da malaman addini masu nagarta a fadin jihar.
Ta kara da cewa gwamnatin jihar ta ware&nbsp Naira miliyan dari bakwai (N700m) wajen taimakawa daukacin daliban da suke karatu a halin yanzu a kasashen Saudiyya da Misira da Kairo don ganin sun kammala karatunsu cikin sauki.
Ta ce kimanin shekaru 16 kenan da&nbsp Jihar ta fada cikin wani mawuyacin hali a fagen ilimi. Ta nuna takaicinta game da yadda harkokin ilimi suka lalace a jihar gaba daya inda ta bayar da tabbacin gwamnati za ta yi bakin kokarinta wajen dawo da martabar ilimi a jihar.
Da yake jawabi Mai martaba Sarkin Dutse wanda Hakimin Shuwarin ya wakilta Alhaji Abbas Sarkin Gabas ya shawarci gwamnatin jihar Jigawa wajen cigaba da daukar nauyin daliban da suka zama zakaru a kowanne fannin rayuwa don su samu ikon yin karatu a awaje.