Jigon Boko Haram da ke da alaka da sace ’yan matan Chibok ya shiga hannu

A Wani jigon kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo mai suna Jarasu Shira ya shiga hannu a shekaranjiya Laraba a garin Damboa.Jaridar Aminiya ta samu labarin cewa wanda ake zargin da ake yi wa lakabi da Jarido an kama shi ne a wata tashar mota tare da wasu da ake zargin ’yan […]

Jigon Boko Haram da ke da alaka da sace ’yan matan Chibok ya shiga hannu
Jigon Boko Haram da ke da alaka da sace ’yan matan Chibok ya shiga hannu

A Wani jigon kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo mai suna Jarasu Shira ya shiga hannu a shekaranjiya Laraba a garin Damboa.
Jaridar Aminiya ta samu labarin cewa wanda ake zargin da ake yi wa lakabi da Jarido an kama shi ne a wata tashar mota tare da wasu da ake zargin ’yan Boko Haram ne su 10 da suka yi masa rakiya zuwa Damboa don hawa mota zuwa Biu.
’Yan aikin sa-kai da ake kira da sibiliyan JTF da suka tallafa wa sojoji a yakin da suke yi da Boko Haram a Arewa maso Gabas ne suka kama ’yan ta’addan da ake zargi.
Shira wanda aka ce shi ne mutum na farko a jerin sunayen ’yan Boko Haram da sojoji k enema ruwa a jallo, Aminiya ta samu labarin cewa ya yi shigar Turawa masu kiwon shanu (Kaboyi) domin batar da kama, amma tsananin sanya ido na ’yan sa-kan na JTF ya sa suka gano shi.
Wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta saboda ba a ba ta damar ta yi magana kan kamen ba, ta shaida wa Aminiya cewa wanda ake zargin yana kan hanyarsa ta zuwa Legas ne.
An hakkake shi ne jagoran kungiyar Boko Haram a kananan hukumomin Damboa da Chibok da Askira Uba da ke Jihar Borno. Majiyar ta ce kuma yana daga cikin manyan ’yan Boko Haram.
An ce yana da karfin fada-a-ji a kungiyar, kuma akwai alamun yana da masaniya kan inda ake ajiye da ’yan matan Chibok da aka sace daga makaranta a watan Afrilun shekarar 2014.
Hedkwatar Tsaro da ke Abuja ta tabbatar da kamun a shekaranjiya Laraba, inda Kakakin Hedkwatar Birgediya Janar Rabe Abubakar ya ce kama Shira ba abin mamaki ba ne, saboda hukumomin tsaro na ta kama ’yan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
Birgediya Janar Rabe ya shaida wa Aminiya cewa, kama ’yan Boko Haram a Arewa maso Gabas na samuwa ne sakamakon sabon hadin gwiwar da ke akwai a tsakanin hukumomin tsaro.
Ya ce ana wadannan kame-kame ne a daidai lokacin da wadanda ake zargin suke zuwa tashoshin mota da sauran hanyoyi a kokarinsu na gudu daga Arewa maso Gabas zuwa ‘wuraren da ake zaune lafiya.’
Aminiya ta samu bayanin cewa an mika wanda ake zargin ga hukumomin soji da ke Biu a Jihar Borno.